Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

A Kasar Maldives Ana Nan Ana tabka Rikici Kan Yinkurin Tsige Shugaban Kasa


Shugaban Maldives Abdulla Yameen
Shugaban Maldives Abdulla Yameen

Ga dukkan alamu muddun 'yan siyasar kasar Maldives ba su yi kaffa-kaffa da takaddamar da ake yi kan makomar Shugaban kasar Abdullah Yameen ba kasar za ta fada cikin wata babbar rigimar siyasa. A yanzu dai kawunan magabatan kasar sun rabu game da bukatun tsige Shugaban kasar.

Kasar Maldives, wacce tsibiri ce, ta abka cikin dambarwar siyasa.

Gwamnati ta gargadi cibiyoyinta da su yi biris da duk wani kira daga kotun kolin kasar, na tsige Shugaban kasar Abdullah Yameen.

“Duk wani umurni daga kotun koli na kama Shugaban kasa zai kasance mai saba ma kundin tsarin mulkin kasa kuma mara hurumi,” a cewar Attoni-Janar din shari’ar kasar Mohammed Anil a yau dinnan Lahadi a wani jawabinsa da aka yada a gidan talabijin din kasar.

A makon jiya kotun kolin ta bayar da umurnin sakin wasu ‘yan adawar siyasa su 9 da kuma wasu ‘yan majalisar dokoki 12 da ke adawa da Shugaban kasar, ciki har da tsohon Shugaban kasa Mohammed Nasheed da ke gudun hijira a kasar waje. Nasheed ne shugaban kasar na farko da aka zaba a dimokaradiyyance.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG