Accessibility links

A Mali 'Yan Tawaye Na Kungiyar Ansar Dine,Sun Kwace Garin Kona, Daga Hanun Gwamnati.


Mali - mayakan sakai na kungiyar Ansar Dine.
A Mali, Shaidun gani da ido sun bada labarin cewa mayakan sakai masu ikirarin Islama sun kwace wani gari daga hanun sojojin gwamnati a tsakiyar kasar.

Wani kakakin kungiyar ‘yan tawayen na kungiyar Ansar Dine, ya ce da misalin karfe 11 na safe agogon Mali, mayakan sakai masu da’awar Islama sun kwace garin Konna. Kuma mazauna garin sun gasgantawa wakilin Muriyar Amurka a sashen faranshi, aukuwar lamarin.

Sojojin daga rundunar Mali sun kara da ‘yan tawayeb kusa da Konna jiya laraba da kuma a yau Alhamis, a lokacinda aka fara ganin alamun mayakan sakai masu kishin addini wadanda suke rike da arewacin kasar suna kokarin kutsawa ta kudanci da ahalin yanzu yake hanun gwamnati.

Garin konna yana tazarar kilomita 45 daga birnin Mopti, inda nan tungar gwamnati ce.

Da yake magana da Muriyar Amurka a yau wani jami’in ma’aikatar tsaron kasar, Kanal Diarran Kone, ya musanta cewa ‘yan tawayen sun kama garin na kona. Kamar yadda ya fada cikin kalamansa, rundunar mayakan Mali, "suna farautar ‘yan tawayen, sai dai yaki ya bayyana shirin sojoji" a wannan gwabzawar da suke yi.
XS
SM
MD
LG