Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Shugaba Morsi ,Ya Ayyana 15 Ga Disemba Domib Kuri'ar Raba Gardama.


Shugaban Masar Mohammed Morsi.

Shugaban Masar Mohammed Morsi ya ayyahna ranar 15 ga watan Disemba domin a yi zaben kuri’ar raba gardama kan sabon daftarin tsarin mulkin kasar, wanda ya janyo rarrabuwar kawuna da kuma zanga zanga masu karfi.

shugaba Morsi ya ayyana ranar ce, bayanda wakilan majalisar da ta rubuta tsarin mulki wacce masu ra’ayin addini suka mamaye ta, suka mika masa kofin daftarin a daren Asabar.

Daftarin tsarin mulkin bai canza manufofin kasar na dogaro kan tafarkin Islama a matsayin hukunce hukuncen kasar.

Tunda farko a jiya Asabar, dubun dubtan ‘yan kasar masu goyon bayan tafarkin addini suka yi zanga zangar nuna goyon bayansu ga shugaba Morsi d a kuma sabon daftarin tsarin mulkin. Gungun mutanen sun hallara ne a harabar jami’ar Alhakira d a kuma a wasu wurare suna kada tutoci, da kellaye da hotuna suna neman a aiwatar da abund a suka kira “dokokin Allah.” Kungiyar da ake kira ta “Yak u ‘yan ‘yan uwa musulmi ne ta shirya gangamin.
A wannan hoto ana ganin magoya bayan shugaba Morsi ne suke zanga zangar nuna goyon baya.
A wannan hoto ana ganin magoya bayan shugaba Morsi ne suke zanga zangar nuna goyon baya.

Haka ma a jiya Asabar din dubban ‘yan Masar din ne suka yi zanga zanga a wuni na tara a jere a dandalin Tahiri domin nuna adawa kan shugaba Morsi da kuma sabon daftarin tsarin
'Yan adawa da shugaba Morsi suke nasu zanga zangar a dandalin Tahrir
'Yan adawa da shugaba Morsi suke nasu zanga zangar a dandalin Tahrir
mulkin kasar.
XS
SM
MD
LG