Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Ana Sa Ran Jirgin Saman Najeriya Zai Soma Jigila A Watan Afrilun Shekarar 2022


Sabuwan jirgin saman Najeriya
Sabuwan jirgin saman Najeriya

Ministan Ma’aikatar, Hadi Sirika ne ya tabbatar da hakan a tattaunarwarsa da manema labarai bayan zaman Majalisar Zartarwa wanda Shugaban Muhammadu Buhari ya jagoranta a ranar Laraba

Ya ce kamfanin Jirgin saman kasar, wanda Gwamnatin Tarayya ce za ta dauki nauyin kulawar da shi da kaso 5 cikin 100, yayin da ’yan kasuwa a kasar za su rike kashi 46 cikin 100, sannan kuma ragowar kashi 49 cikin 100 zai kasance a karkashin wasu abokanan hulda da hadin gwiwa da ya zuwa yanzu ba a mika musu ragamar ba, ciki har da masu zuba hannayen jari daga kasashen ketare.

Ministan ya ce an cimma matsayar kaddamar da kamfanin jirgin saman na Najeriya ne bayan jinkirin da aka rika samu wanda kusan sau biyar ana dakatar da shirin kafa kamfanin sufurin jrgin sama na gwamnatin kasar.

Ministan Sufurin Jiragen Saman Najeriya Hadi Sirika
Ministan Sufurin Jiragen Saman Najeriya Hadi Sirika

Ya kuma kara da cewar yunkurin hakan na zuwa ne jim kadan bayan hawarsa kujerar Minista a shekarar 2015 inda ya kaddamar da taswirar bunkasa harkokin sufurin jiragen sama wanda ya hada da sabon tsarin sufurin jiragen sama da sauran ayyukan da suka shafi harkokin sufurin jiragen sama na kasar a matsayin abubuwan da ma’aikatarsa ta sa gaba.

Ana sa ran batun farfado da kamfani jiragen saman na Najeriya tare da hadin gwiwar ’yan kasuwa zai maye gurbin durkusheshshen kamfanin jirgin sama na Nigeria Airways, wanda ya daina aiki tun a 2003, saboda wasu dalilai da ke da nasaba da sakaci daga bangaren gwamnati wajen kula da lafiyar jiragen da kuma sakaci da aiki daga ma’aikata.

Ministan ya ce wannan ita ce hanyar da ta fi dacewa da za a dauki lokaci ana cin moriyarta, ya kuma ce idan kamfanin ya fara aiki, zai samar da ayyukan yi kusan 70,000 ga ’yan Najeriya.

Ana iya tuna cewa, a watan Yulin shekarar 2018 ne gwamnatin Najeriyar ta kaddamar da suna da kuma tambarin sabon kamfanin sufurin jirgin saman nata wanda rahotonin su ka yi ta yawo cewar an kashe kusan miliyan 80 wajen yi a lokacin bikin baje koli da Ministan ya halarta a birnin Landan, batun da ya karyata da cewa Naira Miliyan 10 aka kashe wajen zana tambarin.

XS
SM
MD
LG