Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

A Najeriya An Kashe Akalla Mutane Fiye Da 20 A Maiduguri.


A wannan hoto ana ganin gawarwaki akan titi, a tashe tashen hankulan baya d a suka addabi musamman arewacin Najeriya.
A Najeriya- shaidun gani da ido a Maiduguri babban birnin jihar Borno dake arewa maso gabashin kasar, sun ce an kashe akalla mutane 21 cikin kwanaki biyu da suka wuce a birnin, yayinda dakarun gwamnati suke cigaba da kai farmaki kan mayakan sakai na kungiyar Boko Haram.

Gwamnati tace an kashe akalla mayakan sakai takwas a birnin ranar Alhamis da ta shige. Ana zaton cewa kisan da aka yi ranar jumma’a, ramuwar gayya ce kan mutane da mayakan sakan suke zargi suna taimakawa dakaru wajen gane mayakan sakai.

Kafofin yada labarai a Najeriya dama na kasashen yammacin duniya sun ce, mayakan sakan sun yi fasakorin shigo da makaman da suka yi amfani dasu a harin nan ranar jumma ne cikin akwatunan daukar gawa, ta haka suka wuce dasu a wuraren da jami’an tsaro suke shinge hanyoyi.

Babu damar a tantance bayanai da gwamnati ko ‘yan tawayen suka bayar, saboda an toshe layukan tarho, kuma an hana manema labarai kaiwa ga inda ake bata kashin a arewacin kasar.

Shin PI Za Ta Fashe Kuwa Ko Yaudara Ce Kawai?

Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG