Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

A Najeriya Yau Shirin Samarwa Matasa Dubu 200 Zai Fara Aiki


ABUJA: Solomon Dalung Ministan Wasanni da Matasan Najeriya
ABUJA: Solomon Dalung Ministan Wasanni da Matasan Najeriya

A yau ne shirin gwamnatin Najeriya na samawar da aikin yi ga matasa kimanin dubu 200 ta bangaren koyarwa da harkar gona da kuma bangaren lafiya zai fara aiki.

Gwamnatin Najeriya ta bayyana cewa nan gaba kadan zata fito da wani tsari na samar da aikin yi ta bangaren wasanni baya ga aikin da zata bayar na mallaman makaranta da malaman gona da kiwon lafiya.

Ministan Matasa da wasanni na Najeriya Barista Solomon Dalung, yace akwai hanyoyin samar da aiki da yawa a bangaren wasanni, wadda kuma ta zamanto hanya mafi sauki wajen samarwa da matasa aikin yi. Ya kuma tabbatar da cewa gwamnati zata bunkasa harkar wasanni.

A karkashin shirin dai za a rika biyan wadannan matasa albashi yayin da suke aikin koyarwa kafin su samu aiki.

Wannan shiri dai daya ne daga cikin shirye-shiryen da gwamnatin Najeriyar ta yi alkawarin aiwatarwa don inganta rayuwar al'ummar kasar.

Domin karin bayani.

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:43 0:00

Hawan Nasarawa, jihar Kano a Najeriya, lokacin da aka gudanar da bukukuwan Sallar Eid el Fitr
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:44 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG