Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

A Nijar An Shawo Kan Cutar Dabbobi da Ta Barke A Jihar Tawa


Firayim Ministan Nijar Birji Rafini

An shawo kan cutar dabbobi a Nijar wadda ta bayyana a kasar a watan Satumbar bara a cikin jihar Tawa

Ministan kiwon lafiya na Nijar Dr. Idi Kallal Mainasara ya bayyana hakan lokacin da suka ziyarci firayim ministan kasar Birji Rafini.

Yace an zo karshen cutar sanadiyar irin matakan da aka dauka da suka kaiga shawo kanta. Goyon bayan da gwamnati ta bayar tare da Majalisar Dinkin Duniya suka taimaka ainun. Yanzu dai babu wani mutum da yake dauke da cutar a duk fadin kasar.

Duk da shawo kan cutar Dr Mainasara yace ana cigaba da daukan matakai da zasu tabbatar cutar bata sake barkewa ba cikin kasar.

Yanzu manoma da makiyaya na iya cigaba da harkokinsu na yau da kullum.

Ga rahoton Haruna Maman Barma da karin bayani.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:15 0:00

XS
SM
MD
LG