Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

A Nijar Hadakar Kungiyoyin Fararen Hula Sun Zargi Wadanda Suka Yi Zanga-zanga Watan Jiya Cewa 'Yan Siyasa Ne


Shugaban Nijar Issoufou Mahamadou

Watan jiya ne wasu da suka kira kansu kungiyoyin fararen hula masu zaman kansu suka gudanar da wata zanga-zangar kin jinin gwamnatin kasar da shugaba Issoufou Mahammadou ke jagoranta

Kungiyoyin fararen hula da suka dunkule sun fitar da wata sanarwa inda suka yi Allah wadai da takwarorinsu da suka gudanar da zanga zanga ranar ishirin ga watan Disambar bara.

Daga bisani jam'iyyun dake mulki sun zargesu da cewa 'yan siyasan adawar kasar ne suka labe da sunan kungiyoyin fararen hula suka gudanar da zanga zangar kin jinin gwamnatin kasar. Su ma sun mayar da martani da tasu zanga zangar ranar 13 ga wannan watan.

Hadakar kungiyoyin fararen hulan da suka fitar da sanarwar baya bayan nan sun zargi wadanda suka yi zanga-zangar watan jiya da cewa 'yan siyasa ne. Kana sun zargesu da neman maida hannun agogo baya game da tafiyar dimokradiya a kasar.

Malam Lawali Adamu mai magana da yawun hadakar kungiyoyin yace kwanakin baya kasarsu ta fuskanci wasu matsaloli dake da nasaba da tada zaune tsaye sanadiyar zanga zangar watan jiya. Yace saboda haka ne a matsayinsu na masu kare dimokradiya suka fito suka ce abun da suka yi bai kamata ba. Inji shi idan kasa na tafiya ba da zanga zanga da tashin hankali ba ake samun masalaha. Kamata yayi bangarori daban daban da lamuran suka shafa su zauna tattauna. Domin hakan sun yi Allah wadai da neman sulhu ta hanyar tada hankali.

Malam Lawali yace su ne suka nemo dimokradiya tare da zubar da jini kafin ta kafu kuma ba zasu sa ido ba su bar wasu 'yan siyasa su yi anfani da sunansu su tada zaune tsaye su rusa dimokradiyar da aka kafa.

Amma su wadanda suka yi zanga zangar watan jiya sun mayarda martani suna cewa su ne kungiyoyin fararen hula kuma zasu cigaba da zanga zanga domin jawo hankalin gwamnatin Nijar kan matsalolin da kasar ke fuskanta. Sun kuma yi watsi da cewa da sunan siyasa suka gudanar da zanga zangar.

Ga rahoton Haruna Mamman Bako da karin bayani.

please wait

No media source currently available

0:00 0:04:05 0:00

XS
SM
MD
LG