Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

A Nijar Jama'a Na Bayyana Alhininsu Kan Rasuwar Tsohon Sarkin Musulmi Ibrahim Dasuki


Tsohon Sarkin Muslmi Ibrahim Dasuki
Tsohon Sarkin Muslmi Ibrahim Dasuki

Yayinda jama'a ke kwararawa daga Jamhuriyar Nijar zuwa Sokoto domin kai gaisuwar ta'aziya saboda rasuwar tsohon sarkin musulmi Ibrahim Dasuki su ko al'ummar Kawanni dake kan iyaka da kasar Najeriya alhininsu suka dinga bayyanawa

Wani Malam Muhammadu Dan Wazifa, babban malami a birnin Kwanni garin da shi ne na farko da Mujaddadi Usmanu Dan Fodio ya kaddamar da rumfarsa yayinda ya soma jihadi domin tabbatar da addinin Islama.

Yace babu abun da zai ce illa ya amince da abun da Allah ya zartar saboda duka mai rai sai ya mutu. Kowa akwai wa'adin da Allah ya diba masa kuma babu mai wuce lokacinsa. Yayi fatar Allah ya jikansa ya kuma gafarta masa.

Jama'ar birni na cikin alhini da juyayin rashin mai alfarma sarkin musulmi na goma sha takwas Ibrahim Dasuki. Dama al'ummar birnin Kwanni sun san marigayin sosai. Mutane da yawa ne suka yiwa sarkin addu'ar neman masa gafara ga Ubangiji.

Ga rahoton Haruna Mamman Bako da karin bayani.

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:56 0:00

XS
SM
MD
LG