Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

A Nijar Kotu Ta Fara Shari'ar Masu Adawa Da Dokar Haraji Ta 2018.


 Nouhou Arzika da lauyoyinsa kan hanyar zuwa kotu a Yamai
Nouhou Arzika da lauyoyinsa kan hanyar zuwa kotu a Yamai

Kotun Yamai a jamhuriyar Nijar ta fara shari'ar masu adawa, irinsu Nouhou Arzika dake turjiya akan sabuwar dokar haraji da suka yi zanga zangar da mahukumtar kasar suka ce bata kan ka'ida

Kotun birnin Yamai ta bude zamanta jiya da shari'ar shugaban kungiyar MPCN Nouhou Arzika, da 'yan fafutikan da aka cafke saboda zarginsu da gudanar da zanga zanga ba kan ka'ida ba.

A karshen makon jiya lauyoyin dake kare 'yan gwagwarmayar suka nuna damuwa akan yadda ake jan kafa wajen soma gabatar dasu gaban alkali domin sanin zahirin laifin da ake zarginsu dashi. Dalili ke nan da lauyoyin ke ganin matakin kotun tamkar wani ci gaba ne kamar yada mai magana da yawun su Martin Sesay Umaru Abdulsalam.

A cewarsa mahukumtar kasar sun ji kiran da suka yi. Can baya lauyoyin sun ce basu amince da alkalin da aka ba shari'ar ba, saboda haka yau sun ga sabon alkali kuma sun amince dashi.

Gabatar da masu fafutikar a gaban shari'a wani mataki ne da ya faranta ran takwarorinsu irinsu Abdulnasir Saidu na NPCR. Kazalika ya ce abu ne ma dake karfafa masu guiwa a ci gaba da kokawar da suka sa gaba. Ya ce su basa tsoron fuskantar shari'a, abunda ba sa so shi ne a yiwa shari'a karan tsaye. Har gobe suna adawa da dokar nan da suke son a kawar saboda zata cutar da jama'a. Abdulnasir yace ya kamata gwamnati ta tausayawa al'ummar kasar ganin irin halin kuncin da suke ciki,amma ba ta kuntata masu da haraji ba.

Bayan an saurare su an mayar da Nouhou Arzika da sauran mutanen da aka cafke ranar 25 na watan Maris zuwa kurkukun Tillabery, yayinda a jiya Litinin, shugaban kungiyar fafutuka da ake kira Wataba Ali Idrisa, dake tsare a gidan kason Filinge, zai bayyana a kotun Yamai. Haka za'a rika jin jami'an dake tsare daya bayan daya har zuwa Juma'a mai zuwa.

Ga rahoton Souley Barma da karin bayani

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:09 0:00

Facebook Forum

Hawan Nasarawa, jihar Kano a Najeriya, lokacin da aka gudanar da bukukuwan Sallar Eid el Fitr
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:44 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG