Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

A Nijar 'Yansandan Yamai Sun Cafke Wasu Masu Fashi da Makami


Wadanda 'yansandan Yamai, Nijar suka cafke bisa zargin suna fashi da makami da muamala da muggan kwaya

Sanadiyar korafe korafen da mazauna Yamai ke yi akan matsalar tsaro, yawan sace sace da makami, da safarar miyagun kwayoyi suka harzuka 'yansandan Yamai yakar wadandan dabiun da tuni suka lakume rayuka da dama a birnin cikin wannan shekarar kamar yadda kakakin 'yansandan birnin Adili Toro ya shaida

Yawan fashi da makami da kashe kashen mutane a birnin Yamai ya sa 'yansanda suka dukufa wurin kawar da wadannan miyagun dabi'u.

Kakakin 'yansandan Yamai Keftain Mainasara Adili Toro shi ya yiwa manema labarai bayani akan yawan mutanen da aka hallaka tun daga farkon wannan shekarar.

Mainasara Adili Toro, kakakin rundunar 'yansandan birnin Yamai
Mainasara Adili Toro, kakakin rundunar 'yansandan birnin Yamai

Yana mai cewa an samu mutane 11 da aka kashe cikin birnin Yamai. Uku cikinsu a gidajensu aka kashesu yayinda barayi suka kutsa gidansu su yi masu sata.

Bayanai daga 'yansanda sun yi nuni da cewa abubuwan dake faruwa a unguwar Kwaratagi, cikin Yamai, nada da halayyar 'yan daba saboda Adili Toro yace mutane shida da aka kashe a unguwar, uku cikinsu fada ne ya shiga tsaninsu.

Acewar Adili Toro wata uku zuwa yau jami'an tsaro sun cigaba da yin sintiri a unguwar kuma sun samu sun cafke mutane 700. Cikin mutanen 'yansanda sun samu wadanda ake tuhumarsu da laifuka da dama.

Kungiyoyin dake yaki da shan miyagun kwayoyi na alakanta kashe kashen mutane da sace sacen dukiyoyin jama'a da yadda matasa suka tsunduma da shan kwaya.

Malam Ganda Saleh shugaban kungiyar "A Daina" yana mai cewa duk inda aka samu kashe kashe tsakanin samari, a tabbata suna fataucin miyagun kwayoyi ne. Haka kuma idan sun yi sata wajen raba kayan da suka sato, rigima na iya barkewa har ta kai ga suna kashe junansu.

A taron manema labarai 'yansanda sun gabatar da mutane takwas da suka ce ana zarginsu da aikata laifin kisan kai.

To saidai masana sun ce samarwa matasa ayyukan yi ne kadai zai karkata hankulansu daga aikata ayyukan asha.

Ga rahoton Souley Barma da karin bayani.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:16 0:00

Facebook Forum

Laftanar Janar Farouk Yahaya

Makasan Sheikh Goni Aisami Sun Bata Sunan Sojin Najeriya – Laftanar Janar Farouk Yahaya
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:11 0:00
Karin bayani akan Bidiyo

Shin da gaske NNPP ba ta yi wa Shekarau adalci ba?

Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG