Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

A saboda munancewar matsalar fari, kungiyar Al Shaba ta Somaliya zata yi na'am da taimako daga kowace kungiya


Wasu yan kasar Somaliya ne a harabar wani sansanin wadanda suka rasa matsuguninsu a bayan da suka arce daga gabashin kasar.

Daya daga cikin fari mafi muni wadda rabon da kasashen gabashin Afrika suka irinta tun shekaru da dama da suka shige, tasa kungiyar yan yakin sa kan kasar Smaliya ta Al Shabab, canja tunanin ta akan kungiyoyin agaji na kasa da kasa.

Fari mafi muni, wadda rabon da aga irinta a yankin gabashin Afrika, tun shekaru da dama da suka shige, tasa kungiyar yan yakin sa kan Al Shabab ta Somaliya canja tunaninta gameda kungiyoyin agaji na kasa da kasa.

Kungiyar Al Shabab tace zata yi maraba da dukkan kungiyoyin agaji, har da wadanda bana Musulmi bane, domin su baiwa mutane da suke zaune a yankunan da suke karkashin ikonta, agajin kayayyakin abinci da wasu kayayyakin.

Mai magana da yawur kungiyar, Sheikh Ali Mahammed Rage ya fadawa yan jarida a birnin Mogadishu a ranar talata da dare cewa, kungiyar zata bari dukkan kungiyoyin agaji shiga kasar, matsawar sun fara tuntunbar kwamitin nazarin fari da kungiyar Al Shabab din ta kafa, kuma ya zamana burinsu shine na bada agajin jin kai.

Ma'aikatar harkokin wajen Amirka ta fada a jiya Laraba cewa, tana da niyar gwada wannan aniya. Sakatariyar harkokin wajen Airka Hillary Clinton tayi wani taro da manyan jami'an ma'aikatar da kuma na kungiyar raya kasashe masu tasowa domin tattauna matsalar fari a yankin gabashin Afrika.

Wani baban jami'i yace, Hillary Clinton ta bada umarnin cewa a dauki dukkan matakin daya dace domin kaucewa aukuwar bala'in jin kai a yankin.

A baya dai, kungiyar Al Shabab ta haramtawa kungiyoyin agaji shiga yankunan da suke hannunta, tana mai fadin cewa zasu ruruta akidar da suka sabawa addinin Musulunci. A bara ne kuma shirin sama da wadatar abinci ta dakatar da aiyukan da yake yi a wasu yankunan kasar Somaliya a saboda barazanar kungiyar Al Shabab.

XS
SM
MD
LG