Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

A Shirye Mu Ke, Ko Da Zabe Zai Kai Zagaye Na Biyu – Farfesa Mahmood


Shugaban hukumar zabe ta INEC a Najeriya, Farfesa Mahmood Yakubu
Shugaban hukumar zabe ta INEC a Najeriya, Farfesa Mahmood Yakubu

Farfesa Mahmood ya kara da cewa, sauyin da aka yi wa dokokin zabe, ya kara saukaka yadda za a gudanar da zaben a zagaye na biyu.

Hukumar zabe mai zaman kanta ta INEC a Najeriya, ta ce ta shirya tsaf ko da zaben shugaban kasa zai kai zagaye na biyu.

Shugaban hukumar Farfsesa Mahmood Yakubu ne ya bayyana hakan yayin da yake gabatar da jawabinsa a Cibiyar “Chatham House” da ke London a kasar Birtaniya, kan irin shirin da hukumar ta yi don gudanar da zaben 2023.

Chatham House, cibiya ce da ke bincike kan al’amuran da suka shafi manufofin kasashen duniya a fannin siyasa, tattalin arziki, ilimi da shugabanci da sauransu.

“Duk zabukan da muka shirya guda uku a baya, mun shirya tsaf don gudanar da zaben shugaban kasa a zagaye na biyu – ko da hakan za ta faru. In hakan ta faru, ba mu da matsala.” Farfesa Mahmood ya ce.

Farfesa Mahmood ya kara da cewa, sauyin da aka yi wa dokokin zabe a Najeriya, ya kara taimakawa wajen gudanar da zaben a zagayen na biyu cikin sauki.

“An kara tsawaita wa’adin gudanar da zaben na zagaye na biyu, daga mako daya zuwa makonni uku, amma kuma da ma, a ko da yaushe, mu kan zauna cikin shiri ko da hakan za ta faru.” Shugaban hukumar ta INEC ya ce, a lokacin da yake amsa tambayoyi bayan gabatar da jawabinsa.

Shugaban hukumar ya kuma kore batun da wasu ke yadawa cewa za a yi amfani da ma’aikatan kananan hukumomi a maimakon farfesoshi na jami’a a matsayin malaman zabe a jihohi.

“Ba za mu iya amfani da ma’aikatan kananan hukumomi ba, ai ba zaben kananan hukumomi mu ke yi ba, akwai tsari da muke bi, kuma wannan tsari bai sauya ba.” In ji Mahmood.

XS
SM
MD
LG