Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

A Somalia Wata Kotun Soji Ta Yankewa Wasu 'Yan Kungiyar al-Shabab Hukuncin Kisa


Shugaban Somalia Mohamed Abdullahi Farmajo
Shugaban Somalia Mohamed Abdullahi Farmajo

Wata kotun soja dake garin Bosaso a arewacin Somaliya, ta yanke ma wasu 'yan al-Shabab hukuncin kisa jiya Litini.

Abdifatah Haji Aden, Shugaban Kotun Soja da ke Puntland, ya ce an tabbatar cewa 'yan bindigar na cikin wadanda su ka yi ta rutsawa da wasu manyan jami'an gwamnati a yankin na Putland wadanda suka yiwa kisan gilla.

"Bayan sauraron ba'asin da kotu ta yi, da kuma gabatar da hujjoji, kotu ta yanke ma wadannan mutane 7 hukuncin kisa," a cewar Aden. "Su na iya daukaka kara cikin kwanaki 30 idan ko ba haka ba za a zartas ta hukuncin."

XS
SM
MD
LG