Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

A Sudan ta Kudu An Samu Sulhu Tsakanin Shugaban Kasar da Shugaban Ma'aikatan Fadarsa


Shugaban Sudan ta Kudu Salva Kiir

Saura kiris Sudan ta Kudu ta sake fadawa cikin wani mummunan tashin hankali biyo bayan sabanin da aka samu tsakanin shugaba Salva Kiir da shugaban ma'aikatar fadar Paul Malong amma aka samu daidaito a wurin addu'a

An yi sulhu tsakanin Shugaban Sudan ta Kudu Salva Kiir da tsohon shugaban ma’aikatan Fadar gwamnatin kasar, mako guda bayan wani kai ruwa rana da aka yi, wanda ya kusa haifar da mummunan fada a Juba, babban Birnin kasar.

Sasantawar ta faru ne a jiya Alhamis a wajen wani taron addu’a da aka yi a Fadar shugaban kasar da ke Juba.

An ga hotuna a shafukan intanet da suka nuna Paul Malong ya rungumi shugaba Kiir.

Gabanin hakan a ranar Alhamis din, wakilin babban Sakatare na Majalisar Dinkin a Sudan ta Kudu, David Shearer, ya yabi gwamnatin Salva Kiir da ta kawo karshen wannan takaddama da aka kwashe mako guda ana yi da Malong.

Shearer ya fadawa manema labarai a ofishin Majalisar Dinkin Duniya da ke Juba cewa, ya na da matukar muhimmancin al’umar Sudan ta Kudu ta sasanta rikicinsu da kansu.

Facebook Forum

Laftanar Janar Farouk Yahaya

Makasan Sheikh Goni Aisami Sun Bata Sunan Sojin Najeriya – Laftanar Janar Farouk Yahaya
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:11 0:00
Karin bayani akan Bidiyo

Shin da gaske NNPP ba ta yi wa Shekarau adalci ba?

Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG