Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Sarakuna A Taraba Sun Yi Kiran A Samu Zaman Lafiya A Yankin Gembu


Gwamna Darius Dickson na jihar Taraba
Gwamna Darius Dickson na jihar Taraba

Biyo bayan irin yawan kashe kashen da suka auku a yankin Gembun jihar Taraba musamman tsakanin manoma da makiyaya sarakunan yankin sun gargadi al'ummominsu da su rungumi zaman lafiya, suyi watsi da makamansu su kuma kiyaye yin kalamun da ka harzuka mutane

Shugabannin gargajiya na yankin Gembu dake jihar Taraba da ya yi fama da tashe-tashen hankula da ya yi sanadiyyar asarar rayuka da dukiyoyin jama’a sun yi kira a kai zuciya nesa don samun dawamammiyar zaman lafiya.

Sarkin Mambila Dokta Shehu Audu Baju na biyu ya furta haka lokacin da yake jawabi a fadarsa inda ya gargadi jama’a su ajiye makamai da daina yin kalamai masu sosa rai ko su fuskanci fushin hukuma tare da tabbacin gwamnati da jami’an tsaro a shirye suke don tsaron lafiya da dukiyoyin jama’a.

Shugaban kungiyar Hausa-Fulani ta raya yankin Gembu Haruna Bakari Tanja ya yi kira da a zauna lafiya kana ya bukaci hukumomin tsaro su tsananta bincike wajen maidowa jama’a dukiyoyin da aka sace ko dauka a matsayin ganima.

Su ma wakilan al’umomi dake fada da juna na Mambila da Fulani Alhaji Umaru Zubairu da Alhaji Saidu Bawa sun yiwa jama’arsu gargadi cewa duk wanda ya dauki ganima sakamakon wannan tashin hankali ya maido da su, tare da bayana masifar da cewa kaddara ce daga Allah.

Jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yansanda ta jihar Taraba ASP David Misal ya ce bayaga harin sari-ka-noke da bangarorin ke kaiwa juna sun yi nasarar kwantar da tashin hankalin.

Wasu mazauna yankin kamar yadda Mohammed Hassan da Mohammed Bugare suka tabbatar wa Muryar Amurka hankula sun kwanta kuma jama’a na gudanar da al’amuran kasuwanci da hada-hadar tattalin arziki a yankin dake kan farfajiyar iyakar Najeriya da jumhuriyar Kamaru.

Saurari karin bayanin rahoton Sanusi Adamu.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:38 0:00

Facebook Forum

Hawan Nasarawa, jihar Kano a Najeriya, lokacin da aka gudanar da bukukuwan Sallar Eid el Fitr
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:44 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG