Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

A Taron G7 Shugaban Amurka Zai Tsaya Kan Harajin Da Ya Dorawa Wasu Kasashe


Larry Kudlow mai ba shugaban Amurka shawara akan harkokin tattalin arziki

Mai ba shugaban Amurka shawara akan harkokin tattalin arziki ya tabbatar cewa shugaban zai tsaya kan harajin da ya kawarawa wasu kasashe a taron G7, wato kasashen da suka fi karfin masana'antu

Daya daga cikin manyan masu baiwa shugaban Amurka shawara akan tattalin arziki Larry Kudlow ya fadawa yan jarida a jiya Laraba cewa shugaba Donald Trump na Amurka zai tsaya akan bakarsa wajen taron kolin kungiyar kasashe masu arzikin masa’antu da ake cewa G7 a takaice, da za’a yi duk da cacakar manufofi harkokin kasuwancin Amurka da kawayen Amurka suka yi ko kuma suke yi.

Mr Kudlow yace galibi akan samu sabanin ra’ayi tsakanin Amurka da sauran kasashe wakilan kungiyar G7. Mr Kudow ya musunta cewa Amurka tana rikici akan harkokin cinnikaya da kawayen ta da kuma China, amma yace Amurka zata dauki duk matakan da suka kamata na kare ma’aikatan Amurka da masana’antunta.

Sakataren tsaron Amurka Jim Mattis a yayinda yake zantawa da yan jaridar a birnin Brussels kasar Belgium a jiya Laraba yace za’a yi garaje ga dami a baiyana rikicin jadawalin kudi fito a zaman rikicin harkokin kasuwanci kuma ya hakake akan cewa Amurka tana da hujjar neman ayi mata adalci a harkokin kasuwanci da kawayen ta.

Facebook Forum

Shin PI Za Ta Fashe Kuwa Ko Yaudara Ce Kawai?

Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG