Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

A Turkiya An Kashe Akalla Jami'an 'Yansanda Uku


Bayan dage dokar hana fita jama'a sun fito suka ga gidaje an yi masu zane da albarusai

Jami'an tsaron kasar Turkiya sun tabbatar da an kashe akalla 'yansanda uku a kasar jiya Lahadi

A kudu maso gabashin kasar Turkiya an kashe akalla jami'an 'yansanda uku a wani mummunan hari biyo bayan rikicin da aka kwashe makonni da dama ana yi tsakanin dakarun gwamnati da mayakan kurdawa.

Majiyoyi biyu sun ce an kashe jami'an 'yansanda biyu cikin wata mota da bom ya tashi kusa da ake binciken ababen hawa a garin Sirnak. Jami'an tsaro sun fatattaki maharan da jirgi mai tashin angulu kuma sun samu nasarar kashe biyu ckinsu yayinda sauran suka arce.

An kashe jami'in 'yansanda na ukun a garin Silvan dake gundumar Diyarbakir bayan 'yan jam'iyyar kurdawa da ake kira Kurdish Workers Party ko PKK a takaice sun kai hari da rokoki.

Cikin makonnin da suka gabata dakarun tsaron Turkiya sun kai hare hare da dama a kudu maso arewacin garin Cizre.

Bayan da aka dage dokar hana fita ta kwana tara mazauna garin sun fito sun ga gidaje da motoci da harsashai suka zanesu kuma koina suka juya fankon albarusai suke gani.

Dalilin Da Ya Sa Nake Sana’ar Sayar Da Shayi Duk Da Cewa Ni Kansila Ne

Dalilin Da Ya Sa Nake Sana’ar Sayar Da Shayi Duk Da Cewa Ni Kansila Ne - Dayyabu Lawal Bala
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:52 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA

Bikin Lasar Gishiri

Yadda Aka Yi Bikin Lasar Gishiri A Jamhuriyar Nijar
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:32 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG