Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

A Yau Lahadi Aka Yi Sallar Azumi A Najeriya


'Yan Najeriya dake arewa maso gabashin kasar, sun yi bikin karamar sallah ranar Lahadi cikin murna da annashuwa da kuma yin addu'o'i
'Yan Najeriya dake arewa maso gabashin kasar, sun yi bikin karamar sallah ranar Lahadi cikin murna da annashuwa da kuma yin addu'o'i

Duk da kalubalen rashin tsaro mutane sun yi tururuwa sun je sallar Idi

Lahadin nan aka yi sallar azumi a Najeriya, kuma duk da yanayin rashin tsaro da hare-haren ba zata da 'yan ta'addan Boko Haram ke kaiwa, al'ummar Musulmi ta yi dafifi ta fita ta yi sallar Idi. A Sokoto duk da cewa ba a yi hawan dabar Salla kamar yadda aka saba ba, bayan sallar Idi Sarkin Musulmi Muhammadu Saad Abubakar na uku ya yiwa al'ummar Musulmin Najeriya jawabin barka da salla inda ya fi maida hankali kan kashe-kashe da rashin tsaron da ya addabi yankin arewacin Najeriya.

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:35 0:00
Shiga Kai Tsaye

A jahar Kano ma al'ummar Musulmi ta yi tururuwa zuwa sallar Idin da Sarkin Kanon Malam Muhammadu Sanusi na biyu ya jagoranta a babban Masallacin Idi na Kano dake kofar mata, kuma Sarkin na Kano ya kara jaddada mahimmancin neman ilimi a cikin hudubar sallar idin da yayi.

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:36 0:00
Shiga Kai Tsaye

Daga bisani kuma majalisar masarautar Kano ta sanar da dakatar da dukkanin haye-hayen al’ada na sarauta albarkacin Salla saboda dalilan tsaro.

A cikin sanarwar da ya gabatar, shugaban kwamitin tsara haye-hayen Salla na Masarautar Kano kuma Hakimin Dala Alhaji Aminu Ado Bayero ya ce majalisar ta dauki wannan mataki ne bisa la'akari da kalubalen tsaro da kasa ke fuskanta.

Haka kuma sanarwar ta bukaci jama'a ta ci gaba da baiwa jami'an tsaro hadin kai wajen gudanar da ayyukan su.

Sai dai kuma a yayin da al'ummar Musulmin Najeriya ke shagulgulan sallar azumi a yau, sauran kasashen da ke makwaftaka da ita kamar su jamahuriyar Nijer, da Kamaru da Ghana sai gobe za su yi salla, kamar mu ma a nan Amurka gobe ne sallar karshen watan azumi na Ramadan.

Wakilan Sashen Hausa a Jahohin Sokoto da Kano, Murtala Faruk Sanyinna da Mahmud Ibrahim Kwari, su ne suka hada rahotannin suka aiko.

XS
SM
MD
LG