Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Abin Da Shugaba Trump Ya Fada a Jawabinsa Kan Coronavirus


Shugaban Amurka, Donald Trump

Yayin da shugaban Amurka ke fuskantar matsin lamba kan bukatar daukar matakai da zasu hana yaduwar cutar Coronavirus, shugaban ya gabatar da wani jawabi wanda aka yada ta gidajen talabijan.

A cikin jawabin nasa wanda yayi kan cutar, ya dauki matakin hana matafiya daga kasashen turai zuwa Amurka na tsawon kwannaki 30.

Duk da dai ya ware kasar Birtaniya daga cikin jerin kasashen Turai din da hanin ya shafa.

Shugaban ya kuma yi amfani da wannan damar wajen mayar wa mutanen da ke zarginsa da kin daukar cutar a matsayin babbar damuwa martani.

Ya ce “muna yin iya kokarin mu domin mu ga mun kare al’ummar kasar Amurka”.

Trump, wanda ya fara gwagwarmayar ganin an sake zabensa a matsayin shugaban Amurka, wanda za a yi ranar 3 ga watan Nuwamba, zai iya amfana da matakan da zai dauka kan cutar wajen samun goyon bayan Amurkawa.

Masana na ganin duk matakin da zai dauka zasu iya taimaka wa siyasarsa ko yi ma ta illa.

Shugaban ya kuma kara da zargin cewa nahiyar Turai na da babban alhakin shigowar cutar Amurka, inda a yanzu mutum 37 ne suka mutu sanadiyyar cutar yayin da 1,281 ke fama da ita.

Ya ce, “Kungiyar Tarayyar Turai ta kasa daukar matakan da suka dace, da kuma hana matafiya zuwa China da sauran wuraren da cutar ta fi kamari. Saboda hakan ne cutar ta samu shigowa Amurka, musamman daga mutanen da suka zo daga nahiyar Turai.”

Hakan na faruwa a ranar da hukumar lafiya ta duniya WHO ta ayyana cutar ta Coronavirus a matsayin wata babbar annoba, yayin da a birnin Washington DC, inda fadar Shugaban Amurka ta ke, aka ayyana dokar ta baci.

Facebook Forum

Melinda Gates

BIDIYO: COVID-19 VOA Ta Yi Hira Da Melinda Gates Kan Dalilin Da Yasa Suke Taimakawa Afirka
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:08 0:00
Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG