Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Abin Da Ya Sa Wasan Najeriya Da Lesotho Zai Zama Tamkar Na Sada Zumunci


Lokacin karawar Najeriya da Benin a Porto Novo (Hoto: Instagram Super Eagles)
Lokacin karawar Najeriya da Benin a Porto Novo (Hoto: Instagram Super Eagles)

‘Yan wasan Crocodiles na kasar Lesotho za su kara da takwarorin wasansu na Super Eagles na Najeriya a wasan neman shiga gasar cin kofin nahiyar Afirka wanda za a yi a Kamaru.

Za a yi karawar ce a filin wasa na Teslim Balogun da ke birnin Legas a kudu maso yammacin Najeriyar.

Sai dai duka kungiyoyin biyu, ba sa bukatar nasarar wasan domin tuni ita Najeriya ta riga ta mallaki gurbinta a gasar, tun kafin ma ta kara da ‘yan wasan Jamhuriyar Benin a ranar Asabar.

Hakan ya faru ne saboda kasar Saliyo sun tashi canjaras a wasansu da Lesothon da za ta gamu da Najeriyar a yau.

Ita kuwa Lesothon ba ta bukatar wannan wasa, saboda ko da ta yi nasara, ba za ta samu damar mallakar gurbi a gasar ba, domin ita ce a karshen teburin wannan rukuni na L.

Malawi ce kasa ta baya-bayan da ta samu gurbin shiga gasar ta AFCON a

Sai Sudan, Ghana, Masar da Gambia, wacce wannan zai zamanto karaonta na farko da za ta je wannan gasa da kuma Zimbabwe wacce za ta je gasar a karo na uku a jere.

Kofin Duniya ta Qatar 2022

Kofin Duniya ta Qatar 2022
please wait

No media source currently available

0:00 0:00:32 0:00
Karin bayani akan Kofin Duniya ta Qatar 2022

Ronaldo vs. Messi

Ronaldo vs. Messi
please wait
Embed

No media source currently available

0:00 0:01:24 0:00
Satumba 30, 2020

Ronaldo vs. Messi

Karin bayani akan Wasanni
XS
SM
MD
LG