Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Abin Da ‘Yan Najeriya Ke Cewa Kan “Tsarin Iyali”


Wasu 'yan Najeriya a layin jefa kuri'a a lokacin zaben 2015

Kididdiga ta nuna cewa adadin 'yan Najeriya ya haura sama da miliyan 190 yayin da Majalisar Dinkin Duniya ta yi hasashen cewa adadin zai haura miliyan 300 nan da shekarar 2050.

A Najeriya, ana ci gaba da ce-ce-ku-ce kan kalaman da wasu rahotanni suka danganta da Ministar Kudi Zainab Ahmed, inda aka ruwaito ta ce hukumomin kasar na duba yiwuwar wani shiri da zai takaita adadin ‘ya’yan da mace za ta haifa a kasar.

Rahotannin sun ce, ministar ta bayyana hakan ne a wani taron tattalin arziki da aka yi a Abuja, inda aka ruwaito ta ce yawan al’umar Najeriya na haifar da cikas wajen samun nasarar shirin farfado da tattalin arzikin Najeriya.

Ko da yake Ministar ta musanta wadannan rahotanni, inda ta ce abin da ta ke nufi shi ne, suna tattaunawa da shugabannin gargajiya da addinai domin yin dubi kan yadda za a kwadaitar da iyalai wajen samun hutun haihuwa.

Wannan lamari ya haifar da ra’ayoyi mabanbanta a tsakanin ‘yan kasar, inda har kwararru a fannin kiwon lafiya suka yi ta tsokaci a kai.

Kididdiga ta nuna cewa adadin 'yan Najeriya ya haura sama da miliyan 190 yayin da Majalisar Dinkin Duniya ta yi hasashen cewa zai haura miliyan 300 nan da shekarar 2050.

Saurari rahoton da Hassan Maina Kaina ya aiko mana daga Abuja:

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:46 0:00

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG