Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Abinda Kauracewa Kamfanonin Afrika Ta Kudu Zai Haifar


Africa xenophobia sign
Africa xenophobia sign

An sami kashe-kashen baki ciki harda 'yan Najeriya a Afrika ta Kudu in da hakan ya ja 'yan Najeriya suka yi zanga-zangar yin Allah wadai da kiyayyar bakin da ‘yan Afrika ta Kudu ke nunawa ‘yan uwansu na Afrika ciki har da ‘yan Najeriya.

Zanga-zangar mutanen Najeriyar na kira ne da a kauracewa dukkan wasu kamfanonin Afrika ta Kudu da suke a Najeriya kamar su MTN, DSTV, SHOPRITE da makamantansu.

Suna ganin yin hakan ne kadai zai iya shafar tattalin arzikin can kasar saboda irin tasirin karauwar da suke yi da ‘yan Najeriya kullum safe ta maganar harkokin sadarwa.

Sai dai wani mai fashin bakin al’amura Dakta Nasir Kurfi yace ‘yan Najeriya ba su da mafita ko makwafin hanyoyin sadarwar da zai iya sawa har su kauracewa na Afrika ta Kudu.

Yace da muna da kamar kamfanonin sadarwar da zasu iya mana abinda muke samu daga na Afrika ta Kudun to da abin zai yi matukar tasiri kuma zai taba tattalin arzikinsu musamman nan gaba.

Game da maganar barazanar MTN na cewa in suka rufe ofishinsu na Najeriya mutane zasu rasa guraben ayyuka, sai yace MTN ba zasu iya rufe kamfaninsu ba don sun kafu ne da kudin da suka samu a Najeriya.

Daga karshe ya nuna cewa ga dukkan alamu gwamnatin Afrika ta Kudu ta damu kasancewar kama mutane sama da 300 a kasar za kuma a kai su kotu game da wannan matsala.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:30 0:00

Hawan Nasarawa, jihar Kano a Najeriya, lokacin da aka gudanar da bukukuwan Sallar Eid el Fitr
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:44 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG