Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

AC Milan Ta Yi Ma Napoli Ci 3-0 A Wasan Lig-Lig Na Serie A


Dan wasan AC Milan, Zlatan Ibrahimovic, bayan da ya jefa kwallo a ragar 'yan Napoli, litinin 28 Fabrairu 2011

Zlatan Ibrahimovic da AC Milan sun nuna cewa ba a banza suke saman kowa a wasannin lig-lig na Serie A na kasar Italiya ba

Tun da aka fara wasa 'yan AC Milan suke kanianaye kwallo, amma sai da aka komo daga hutun rabin lokaci suka samu nasarar jefa kwallaye a ragar 'yan kungiyar Napoli, suka doke su da ci 3-0, abinda ya ba su ratar maki 5 kan abokan hamayyarsu na cikin birnin Milan, watau Inter Milan, a wasannin lig-lig na kasar Italiya, ko Serie A.

Zlatan Ibrahimovic da Kevin-Prince Boateng da kuma Alexandre Pato sun jefa kwallayen a bayan komowa daga hutun rabin lokaci a wannan wasa da aka yi a San Siro.

Ibrahimovic ya jefa kwallon farko ana minti na 49 da fara wasa a bugun fenariti da aka ba 'yan AC Milan bayan da dan wasan baya na Napoli, Salvatore Aronica, ya taba kwallo da hannu. Boateng ya jefa kwallo na biyu a bayan da Pato ya gangaro masa kwallon a minti na 77. Mintoci biyu bayan wannan sai shi Pato dan Brazil ya jefa kwalo na uku.

A yanzu, AC Milan tana saman Serie A da maki 58, sai Inter Milan mai maki 53 a matsayi na biyu, yayin da ita kuma Napoli take matsayi na uku da maki 52.

AC Milan ta kanainaye wasan kafin hutun rabin lokaci, amma ta kasa yin komai saboda 'yan wasan Napoli su na taruwa su na tsare gida. A bayan komowa daga hutun rabin lokacin ma, mai tsaron gida na Napoli, Morgan De Sanctis, ya tare wasu kwallayen da aka dauka za su shiga raga kawai.

A daya bangaren, dan wasan Napoli Edinson Cavani, wanda ya jefa kwallaye har 20 a bana, ya kasa samun kwallon a wasan jiya.

XS
SM
MD
LG