Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Adadin Masu Coronavirus a Najeriya Ya Zuwa Yanzu


Hukumar hana yaduwar cututtuka ta NCDC a Najeriya, ta ce mutum 139 ne aka tabbatar sun kamu da cutar Coronavirus a kasar.

A cikin adadin dai akwai mutum 2 da suka rasa rayukansu, yayin da tara suka warke daga cutar.

Hakan na faruwa a daidai lokacin da yawancin jihohi da biranen kasar suka ayyana dokar zama a gida domin takaita yaduwar cutar.

Hukumar ta bayyana cewa za ta yi amfani da wannan lokacin da kowa yake zaune a gida, domin bin wadanda suka kusance masu dauke da cutar har gida kullum, na tsawon kwannaki 14 domin duba lafiyarsu akai-akai.

A biranen Legas da Abuja da kuma Ogun, inda cutar ta fi kamari, dokar zama a gida wacce shugaban kasar Muhammadu Buhari ya ayyana ta fara aiki a daren Litinin din da ta gabata.

Facebook Forum

Wani Sirri Da Tsohon Shugaban Nijar Mahamadou Issoufou Ya Fadawa ‘Sarki Sanusi II’
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:23 0:00
Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG