Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Adadin wadanda girgizar kasa kashe a Ecuador sun haura sama da 500


Masu aikin ceto suke zakulo mutane daga baraguzan gidajen da suka rushe suka kuma rikito kan mutane

Kasashen duniya suna aikewa da daruruwan miliyoyin dala da masu aikin ceto zuwa Ecuador, yayinda adadin wadanda girgizar kasa mai karfin gaske data auku ranar Asabar, ya haura samada dari biyar.

Jami'an kasar suka ce sai tayiwu wannan adadi ya karu, domin har yanzu akwai mutane fiyeda dari biyu wadanda har yanzu ba'a san inda suke ba.

Masu aikin ceto daga kasashen yankin Pacific suna amfani da wani kayan aiki na zamani, da karnuka, da kuma hannayensu suna tono baraguzan gidaje da shaguna, suna kasa kunne su ji motsin ko akwai wani da rai dake neman a ceto.

An zakulo wasu mutane daransu daga karkashin baraguzan, sai dai hukumomin kasar suka ce kiraye kirayen neman taimako da woyoyin celula da wadanda gine ginen suka danne suna raguwa.

Tuni dama tattalin arzikin kasar yake fuskantar matsanancin komada sabili da faduwar farashin mai a kasuwannin duniya.

Jiya Talata shugaban Amurka Barack Obama, ya bugawa shugaba Correa domin ya mika ta'ziyyar Amurkawa saboda rashin rayukar da girgizar kasar ta haddasa. Ya baiwa shugaban na Ecuador tabbacin Amurka zata yi bakin kokarinta wajen taimakawa kasar ta sake farfadowa.

Nijar, Fulani, Wodaabe

Yadda Funalin Wodaabe Suka Gudanar Da Gasar Nuna Kyau A Nijar
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:22 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA

Sauyin yanayi : Yankin Sahel na Afrika

Yadda Sauyin Yanayi Ke Rura Wutar Rikici A Yankin Sahel
please wait

No media source currently available

0:00 0:12:44 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG