Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Adadin Wadanda Suka Kamu Da COVID-19 a Afrika Ta Kudu Ya Zarta 500,000


Gwajin zafin jiki a Afrika Ta Kudu
Gwajin zafin jiki a Afrika Ta Kudu

A ranar Asabar 1 ga watan Agusta adadin wadanda aka tabbatar sun kamu da cutar COVID-19 ya zarta 500,000 a Afrika ta kudu, adadin da ya zama kaso 50 cikin 100 na wadanda suka kamu da cutar da aka sani a kasashen Afrika 54.

A daren ranar Asabar ministan ma’aikatar lafiya na kasar Zwelini Mkhize ya sanar da cewa an samu karin mutum 10,107 da suka kamu da cutar, abinda ya sa gaba dayan adadin yanzu ya kai 503,290, ciki har da mace-mace 8,153.

Afirka ta Kudu: COVID-19
Afirka ta Kudu: COVID-19

Afrika ta kudu, mai yawan jama’a kusan miliyan 58, ita ce kasa ta 5 a lissafin kasashen da cutar ta fi kamari a duniya, bayan Amurka sai Brazil, Rasha da India, dukkansu kasashe ne da ke da yawan al’umma, a cewar jami’ar Johns Hopkins. Kwararru sun ce ainahin adadin wadanda suka kamu da cutar a fadin duniya ya wuce wanda aka tabbatar, saboda karancin kayayyakin gwaje-gwaje.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG