Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Adadin 'Yan Najeriya da Suka Rasu a Saudiya Ya Karu Zuwa 145


Wasu alhazan Najeriya da suka dawo daga aikin hajjin bana
Wasu alhazan Najeriya da suka dawo daga aikin hajjin bana

Hukumar alhazan Najeriya ta sake bada karin alhazan da suka rasa rayukansu sakamakon turmutsitsin da aka yi a Saudiya ranar 24 ga watan jiya

Kwamishanan labaran hukumar alhazan Najeriya Dr Saleh Okenwa shi ya bayyana karin adadin wadanda suka rasa rayukansu a turmutsistin Saudiya.

Yanzu sun kai dari da arba'in da biyar, wato sun tashi daga tasa'in da tara na alkaluman baya. Har yanzu kuma ana kokarin gano ko tantance mutane 165 da ba'a san inda suke ba ko kuma abun da ya faru dasu.

Shugaban hukumar Alhazan Barrister Abdullahi Muhammad Mukhtar a jawabinsa ya musanta wani bidiyo da ake yayatawa dake nuni da cewa ba'a mutunta gawarwakin wadanda suka mutu ba.

Shugaban yace hukumar tana nan tana bin alkawarin da sarki Salman ya yiwa wadanda naurar gini ta kashesu a masallacin Ka'aba. Ofishin jakadancin Najeriya dake Jeddah zai tabbatar ya karbo ma mutanen hakinsu.

Ga karin bayani.

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:56 0:00
Shiga Kai Tsaye

XS
SM
MD
LG