Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Adamawa: An yiwa wasu yankan rago a garin Madagali


Jihar Adamawa

Wasu 'yanbindiga da ake kyautata zaton 'yan kungiyar Boko Haram ne sun yiwa mutane yankan rago a garin Madagali dake cikin jihar Adamawa

Rahotanni suna cewa wasu 'yan bindiga ne suka shiga butu zuwa cikin garin na Madagali inda suka yiwa wasu yankan rago yayinda aka garzaya da wasu asibiti sakamakon raunuka da suka samu.

Wani mazaunin garin yace da dare 'yan ta'adan suka shiga garin suka kama yanka mutane. Suna bi gida gina suna yanka mutane. Sun kuma jima wasu jiwao. Basu bi layin da sojoji suke ba. Sun bi bayan gari ne ta makabarta inda babu jami'an tsaro suka shiga garin. Kawo yanzu an samu mutane shida da suka yanka.

Banda yanka mutane sun kuma kone manyan gidaje biyu. Rundunar sojin jihar bata yi wani karin haske ba game da lamarin.

Mr Adamu Kamali dan majalisar wakilai mai wakiltar yankin ya tabbatar da faruwar lamarin kuma ya bukaci a kara shigayen soji a yankin kasancewa wurin na kusa da dajin Sambisa inda 'yan Boko Haram suka yi kakagida.

Ga karin bayani.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:57 0:00

Shugaba Joe Biden ya zama Shugaban Amurka na 46

Fashin baki kan rantsarda da shugaba Joseph Biden da Kamala Harris

BIDIYO: Fashin baki kan rantsarda da shugaba Joseph Biden da Kamala Harris
please wait

No media source currently available

0:00 0:06:51 0:00

An rantsar da sabon shugaban Amurka Joe Biden da mataimakiyarsa Kamala Harris

BIDIYO: An rantsar da sabon shugaban Amurka Joe Biden da mataimakiyarsa Kamala Harris
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:35 0:00

Bikin Rantsar da Joseph R. Biden a Matsayin Shugaban Amurka na 46

Bikin Rantsar da Joseph R. Biden a Matsayin Shugaban Amurka na 46
please wait

No media source currently available

0:00 1:45:22 0:00
XS
SM
MD
LG