Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Adamawa: Boko Haram Ta Kone Garin Yumbuli Kurmus


Gwamnan Adamawa Muhammad Jibrila Bindow
Gwamnan Adamawa Muhammad Jibrila Bindow

A wani mummunan hari da Boko Haram ta kai yankin Madagali ta kwashi awa uku tana kone garin Yumbuli inda babu abun da ta bari kuma duk mutanen garin da suka tsere kayan jikinsu ne kawai dasu, garin kuma ya zama toka gaba daya saboda hatta dabbobi basu tsira ba.

Rahotanni da muka samu da dumi duminsu na cewa 'yan kungiyar Boko Haram sun kone garin Yumbuli kurmus.

Garin Yumbuli yana cikin karamar hukumar Madagali ne kuma yana kan iyaka da dajin Sambisa inda 'yan Boko Haram suka yi kakagida.

Harin na yau shi ne na hudu cikin mako guda da 'yan Boko Haram zasu kai a yankin na Madagali.

Shugaban karamar hukumar Madagali shi ya yiwa Muryar Amurka karin bayani daga baya kuma watakila jami'an tsaro zasu bada nasu.

Ta bakin Alhaji Yusuf Muhammad shugaban karamar hukumar Madagali abun da suka tarar abun takaici ne kuma abun kuka ne saboda duk garin gaba daya 'yan Boko Haram suka kone. Sun kone gidagensu da abincinsu da dabbobinsu da duka kayansu. Babu wanda ya fita da komi illa abun da yake sanye dashi.

Alhaji Yusuf yace babu wanda aka kashe saboda duk sun gudu sun hau duwatsu. A jihar Adamawa Madagali ce ta fi shan wahala a hannun 'yan Boko Haram. Kullum sai an kashe mutane a yankin.

Inji Alhaji Yusuf mutanensu basu iya zuwa gona. Ya roki gwamnati ta taimaki mutanensu su kuma kara dakarun tsaro ba jiye sojoji hamsin ba kawai. Yace a kawo sojoji da yawa domn suna makwaftaka da dajin da 'yan ta'addan suke.

Ga rahoton Ibrahim Abdulaziz da karin bayani.

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:07 0:00

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG