Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

ADAMAWA: Civil Defense na kawo sulhu tsakanin Fulani Makiyaya da Manoma


Rundunar Civil Defennse, Jihar Adamawa
Rundunar Civil Defennse, Jihar Adamawa

Yadda rikici ke yawon barkewa tsakanin makiyaya da manoma a jihar Adamawa ya sa rundunar Civil Defense kebe wani reshenta wanda yake kawo sasantawa tasakanin manoma da makiyaya kuma duk bangarorin biyu sun himmatu da aikin rundunar.

Rundunar tsaron farin kaya Civil Defense, reshen jihar Adamawa, dake kawo sulhu tsakanin makiyaya da manoma yana shiga daji ne domin zakulo masu laifi.

Yunkurin na kawo sulhu tsakanin makiyaya da manoma ya soma yin tasiri a jihar Adamawa.

Suleiman Baba jami'in hulda da jama'a a jihar Adamawa, na rundunar shi ya bayyana irin nasarorin da suke samu. A cewarsa bisa umurnin gwamnatin tarayya suka bude sashen dake shiga daji yana zakulo masu laifi, sannan akwai sashen dake kula da dabbobi da gonaki da anfanin gonaki. Akwai kuma bangaren dake warware rikici.

A cewarsa da zarar sun sami masu laifi sai su shiga batun sasantawa. Aikin da suke yi har ya sa sun samu takardar yabo daga gwamnatin jihar. Ya ce suna tare da makiyaya da manoma amma kuma suna son gwamnatin jihar ta zaburo ta sa iyaka tsakanin burtali da filin noma.

Shugabannin kungiyoyin makiyaya su ma sun yi furuci a kai. Alhaji Musa Usman daya cikin shugabannin kungiyar PULAKO ta Fulani, ya ce sau tari 'yan Civil Defense, sun je wurinsa domin sasanta rikici. Ya ce sun sasanta akan gonaki da yawa.

Shi ma Muhammad Baba, wani manomi da shanu suka yiwa barna a Yola, an sasanta dashi ba tare da zuwa gaban shari'a ba.

Sai dai sau tari kananan yara dake kiwo suke haddasa barna a gonaki kuma kusan kowane lokaci yawancinsu na cikin maye sabo da haka aka yi kira ga makiyaya su san irin yaran da suke sa kiwo.

Ga rahoton Ibrahim Abdulaziz da karin bayani

please wait

No media source currently available

0:00 0:04:51 0:00

Facebook Forum

Hawan Nasarawa, jihar Kano a Najeriya, lokacin da aka gudanar da bukukuwan Sallar Eid el Fitr
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:44 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG