Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

ADAMAWA: Dambarwar Siyasa Ta Kunno Kai a Sarautar Jada


Gwamnan jihar Adamawa Muhammad Jibrilla Bindo
Gwamnan jihar Adamawa Muhammad Jibrilla Bindo

Wata sabuwar rikicin siyasa tsakanin masu biyayya ga tsohon mataimakin shugaban kasar Najeriya Alhaji Atiku Abubakar da wata kungiya ta kwankwasiya wadda Walin Ganye Alhaji Sadiq Kalu ke jagoranta ta kunno kai biyo bayan gwagwarmayar kujerar hakimin Jada ta masarautar Ganye da ke jihar Adamawa.

An sami sabani tsakanin bangarorin biyu lokacin da wasu mutane biyu 'yan gida daya suka Shiga takarar kujerar hakimin Jada kuma ko wannensu da bangaren da ke goya masa baya.

Amma ana tsammanin lafawar kura bayan nadin sabon hakimin Jada Alhaji Umar Ardo sai gashi daya daga cikin masu yiwa tsohon shugaban kasa Alhaji Atiku Abubakar, wato Alhaji Mohammed Suleiman Baba Jada ya je kotu inda ya yanki takardar daukar rantsuwa ranar ashirin da shida ta watan Afrilu shekarar nan don gabatar da shaida ga hukumomin tsaro yana zargin Walin Ganye Alhaji Sadiq Kalu da kungiyar kwankwasiya da niyyar tada zaune tsaye ta hanyar harzuka matasan yankin.

Wasikar rantsuwarda Alhaji Suleiman Baba Jada yayi a kotu
Wasikar rantsuwarda Alhaji Suleiman Baba Jada yayi a kotu

Amma Walin Ganye ya musanta zargin. Ya martanin cewa ba shi da wata alaka da kungiyar ta kwankwasiya. Ya hada da cewa kamata ya yi dattawa kaman su Alhaji Mohammed Suleiman Baba Jada su nemi hanyoyin dinke baraka lokacin da aka sami sabanin ra'ayi maimakon kalan maganganu.

Wani mazaunin garin Jada Malam Yahya Dan Maisamari ya tabbatarwa sashin Hausa takarar kujerar hakimin ce ta yi sanadiyyar raba al'ummar musamman matasan Jada gida biyu lamarin da ke da hatsari ga zaman lafiyar yankin.

Ga Karin bayanin daga rahoton Sanusi Adamu.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:16 0:00

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG