Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

ADAMAWA: Hukumar Zabe Tayi Zama da Masu Ruwa da Tsaki Kan Harkokin Zabe


Farfasa Muhammad Yakubu shugaban hukumar zaben Najeriya, INEC
Farfasa Muhammad Yakubu shugaban hukumar zaben Najeriya, INEC

Hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa ta baiwa kutare tabbacin zata samar masu da damar kada kuri’a a zabe mai zuwa na 2019 a tanade-tanaden ta na soma sabunta kain zabe da yin rajistar masu zabe da zata soma ranar ashirin da bakwai ga watan nan wanda ake saran za a dauki tsawon kwanaki casa’in ana yi.

Sakataren gudanarwa na hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa ta jihar Adamawa Malam Salihu Ya’u ya ba da tabbacin haka a taron masu ruwa da tsaki na shugabannin jam’iyun siyasa, jami’an tsaro, kungiyoyin sa ido kan harkar zabe da kafofin yada labarai don nazarin shirye-shiryenta na soma aikin sabunta katunan zabe da rajistar sabbin wasu.

Taron hukumar zabe da masu ruwa da tsaki a Adamawa
Taron hukumar zabe da masu ruwa da tsaki a Adamawa

Wasu daga cikin batuttuwan da mahalarta taron suka nuna damuwa a kai, sune na ‘yan gudun hijira da Boko Haram ta raba da muhallinsu saboda sharudan da hukumar zaben ta gindaya kamin ta sabunta masu katin zabe da kuma kutare da a zaben 2015 da ya gabata ba su sami damar kada kuri’a ba sakamakon rashin tanadi domin su.

Bakin shugaban jam’iyar adawa ta PDP ta jihar Adamawa Barr, Abdulrahaman Bobboi da na sakataren tsare-tsare na jam’iyar APC Alhaji Ahmed Lawan ya zo daya inda suka nemi hukumar zabe ta kasa ta sassauta sharudan da ta gindayawa masu neman sabunta katinsu da kuma kutare don su sami dama kamar kowane dan kasa a zabubbuka masu zuwa.

INEC
INEC

Ofisoshin hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa da ke kananan hukumomi ashirin da daya na jihar Adamawa na gudanar da tarurrukan masu ruwa da tsaki kan harkar soma rajistar masu zabe kana kuma ta kaddamar da gangamin fadakar da al’uma muhimmancin sabunta katin zabe da yi wa masu kada kuri’a rajista ta kafofin yada labarai.

Saurari Karin bayanin rahoton Sanusi Adamu.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:18 0:00

Facebook Forum

Wata manhaja mai saukaka wahalar samun gidan abinci na halal ga Musulman dake zaune a kasashen Turai
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:21 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG