Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Adamawa: Jami’an Tsaro Sun Dakile Yunkurin Kai Hari


Shugaban Masu Aikin Sa Kai Adamu Abdullahi

Rahotanni daga yankin Madagali a jihar Adamawa arewa maso gabashin Najeriya na cewa sojoji da yan sakai na maharba sun dakile wani yunkuri kai hari da wasu ‘yan Boko Haram suka yi yunkurin yi.

Wannan kuma na zuwa ne yayin da al’ummomin yankin ke ci gaba da gudanar da bukukuwan samun zaman lafiya, biyo bayan kwato yankin daga hannun mayakan Boko Haram.

Kamar yadda rahotanni daga yankin na Madagali ke bayyanawa ‘yan bindiga masu tada kayar bayan na kokarin sake kai mummunan farmaki ne, to amma kuma basu taki sa’a ba, inda sojoji da kuma yan sakai na maharba suka yi musu kofar rago.

Wani dan sakai na maharba yace sun yi yunkurin kai harin ne a gefen Waga Chakawa dake kusa da dajin Sambisa, inda yace an kashe mayakan Boko Haram da dama.

Shima kwamandan yan sintiri na vigilante a jihar Adamawa, Adamu Abdullahi ya tabbatar da faruwan lamari da ma irin nasarar da aka samu akan yan kungiyar ta Boko Haram.

Wannan dai na zuwa ne yayin da al’umman ta Madagali ke bukukuwan murnar samun zaman lafiya. To ko yaya al’umman yankin suka ji da wannan yunkuri na Boko Haram. Yusuf Mohammad, dake zama shugaban karamar hukumar ya tabbatar da afkuwar lamarin tare da bayyana hadin kan da ake samu a yanzu.

Al'ummar Madagali Suna Murnar Samun Zaman Lafiya
Al'ummar Madagali Suna Murnar Samun Zaman Lafiya

Madagali dai itace karamar hukumar farko da mayakan Boko Haram suka fara kwacewa a jihar Adamawa, inda suka ci karensu babu babbaka kafin daga bisani dakarun Najeriya suka kwato yankin, wanda kuma kawo yanzu akan dan samu harin sari –ka-noke a wasu lokutan, batun da dan majalisar wakilai mai wakiltar Madagali da Michika Mista Adamu Kamale, ya yi kira da a kara sansanonin soji a yankin.

Domin karin bayani saurari cikakken rahotan Ibrahim Abdul’aziz.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:18 0:00

Facebook Forum

Arewa A Yau

Arewa A Yau
please wait
Embed

No media source currently available

0:00 0:00:47 0:00
XS
SM
MD
LG