Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Adamawa: Ma’aikata Sun Koka Kan Zaftare Musu Albashi


tsoffin ma'aikatan jihar Adamawa

Ma’aikata a jihar Adamawa na kokawa sakamakon zaftare musu albashi domin yin katin shaidar ma’aikata wato ID Card, batun da ma’aikatan suka ce ba zata sabu ba.

Wannan zaftare kudaden na zuwa ne yayin da ma’aikatan kananan hukumomin jihar 21 ke ci gaba da hamma ta rashin samun albashi, inda wasu suka shafe fiye da watanni uku babu albashin.

Kamar yadda bayanai ke nunawa an zaftare albashin ne domin gudanar da aikin katin ma’aikata wato ‘ ID card,’ da kungiyar kwadago a jihar ta bukaci a aiwatar inda kungiyar ta bada umarnin da a cire naira N1,500, koda yake ma’aikatan sunce basu san da wannan batu ba.

Wasu ma’aikatan da suka harzuka sun garzaya ofishin akanta janar na jihar domin neman bahasin zaftare musu kudaden da aka yin a fiye da abin da kungiyar kwadagon ta nema.

Don jin hakikanin abin da ya faru wakilin Muryar Amurka ya leka ofishin akanta janar ta jihar Adamawa, to amma ko hakata bata cimma ruwa ba, domin kuwa suna wani taron gaggawa, haka Muryar Amurka ta tuntubi kwamishinan yada labaran jihar Ahmad Sajo, wanda yace zai tuntube wakilin to amma har lokacin hada wannan rahoto babu labari daga gareshi.

To sai dai kuma, a martaninta kungiyar kwadagon jihar NLC, ta bakin shugabanta Kwamared Dauda Maina, tace ba haka suka tsara tun farko ba.

Ya zuwa yanzu shugabanin kungiyar kwadago sunce zasu gana da bangaren gwamnati don gano bakin zaren magance wannan takaddama, kamar yadda shugaban kungiyar kwadagon yayi Karin haske.

Domin karin bayani ga rahotan Ibrahim Abdul’aziz.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:40 0:00

Facebook Forum

Laftanar Janar Farouk Yahaya

Makasan Sheikh Goni Aisami Sun Bata Sunan Sojin Najeriya – Laftanar Janar Farouk Yahaya
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:11 0:00
Karin bayani akan Bidiyo

Shin da gaske NNPP ba ta yi wa Shekarau adalci ba?

Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG