Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

ADAMAWA: Maharban dake Taimakawa a Yaki da Boko Haram Sun Yi Barazanar Janyewa


mAHARBAN jIHAR aDAMAWA
mAHARBAN jIHAR aDAMAWA

Hadakar kungiyar yan sakai na maharba a Najeriya sun gudanar da wani taron gaggawa a jihar Adamawa don gano hanyoyin magance matsalolin da suka yi mata tarnakaki a yaki da masu tada kayar baya na Boko Haram.

A taron wasu 'ya'an kungiyar da dama sun nemi da ta janye daga bakin daga a taimakawa dakarun sojin Najeriya da 'yan sakan ke yi a yanzu a yaki da 'yan Boko Haram sakamakon abun da suka kira ko in kulan da suke zargin gwamnatocin jihohi ke nuna musu

Yayin dai wannan taron gaggawa da yan sakan na maharba suka gudanar maharban sun koka game da rashin tallafi daga gwamnatocin wasu jihohi duk kuwa da irin taimakon da suke bayarwa a yaki da masu tada kayar baya na Boko Haram.

A dai wajen taron da ya kunshi jihohin arewa maso gabas,wasu yan sakan sun bukaci da su janye daga taimakon da suke badawa.

Wani batu ma dai da aka tabo a wajen wannan taro shine na rashin hadin kai a tsakanin kungiyoyin maharba a Najeriya,batun da sakataren tsare tsare na kungiyar Modibbo Usman ke cewa dole a yi karatun ta natsu.

To ko wane matsayi aka dauka game da batun janyewa daga tallafin da suke badawa a yaki da masu tada kayar baya na Boko Haram.

Alhaji Muhammmad Usman Tola shine shugaban kungiyar maharba na jihohin arewa maso gabas ya baiwa 'yan sakan hakuri tare da kira ga gwamnati da a taimaka.

Su ma dai mata maharba ba’a barsu a bayaba wajen wannan taro.Aisha Bakari Gombi itace kwamandan mata a kungiyar maharban Najeriya,tace suna nan daram.

Shugabar mata maharba
Shugabar mata maharba

Kamar yadda alkalumma ke nunawa yan sakai na maharba da dama ne dai suka rasa rayukansu a yaki da masu tada kayar baya na Boko Haram,batun da manazarta ke ganin akwai bukatar tallafawa.

Ga rahoton Ibrahim Abdulaziz da karin bayani.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:11 0:00

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG