Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Adamawa: Manoman Shinkafa 3000 Za Su Ci Gajiyar Tallafin Miliyan 750


Kayan noman shinkafar rani da za'a ba manoma rance a Adamawa
Kayan noman shinkafar rani da za'a ba manoma rance a Adamawa

Kananan manoma 3,000 na jihar Adamawa ake sa ran za su amfana da shirin samar da rancen Naira Miliyan 750 domin noman shinkafar wanda gwamnatin tarayyar Najeriya za ta bayar.

Karkashin tsarin ba da rancen, kowane manomi zai sami Naira 250,000 don noma kadada daya.

Daga cikin wannan kason na rancen, shirin ya tanadarwa kowannensu taki, maganin feshi, injinan ban ruwa da ingantaccen iri don kaucewa karkata kudaden zuwa biyan wasu bukatu na kansu.

Da yake kaddamar da shirin mataimakin gwamnan jihar Adamawa, Injiniya Martin Nasir Babale ya bayyana aniyar gwamnati na fadada shirin yadda kananan manoma 40,000 za su amfana ta hanyar juya kudaden bayan sun biya rancen.

Daga cikin matakan da shirin ya tanada, domin ganin manomi ya samu riba ko da farashin shinkafan ya fadi a kasuwanni akwai tsarin saye amfanin gonan kai tsaye daga hannun manoman, in ji injiniya Abubakar Aji shugaban hukumar koyar da sabbin dabarun noma ta jihar Adamawa.

Sai dai wasu daga cikin kananan manoman da sashen Hausa ya tuntuba don jin ra’ayinsu kamar irinsu Alhaji Tafida Maikano, a ganinsu an makara wajen kaddamar da shirin ana gab da sauran ‘yan makonni a shiga damina.

Ga rahoton Sanusi Adamu da karin bayani.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:09 0:00

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG