Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

ADAMAWA: Shirin Gwamnati Na Rufe Sansanonin 'Yan Gudun Hijira Ya Janyo Cecekuce


'Yan gudun hijira da za'a rufe sansaninsu

Yayin da hukumomin bada agaji a Najeriya ,ke haramar rufe wasu sansanonin yan gudun hijira a jihar Adamawa arewa maso gabshin Najeriya,wasu yan gudun hijiran na rokon a barsu.

Kamar yadda alkalumma ke nunawa kawo yanzu akwai daruruwan yan gudun hijira da rikicin Boko Haram ya raba da gidajensu dake wasu sansanonin yan gudun hijira da aka tanadar.

To sai dai kuma kawo yanzu hukumomi a jihar Adamawa daya daga cikin jihohin da rikicin Boko Haram yayiwa tu’annati na shirin rufe sansanonin dake jihar,batun da wasu yan gudun hijira ke ganin akwai abun dubawa.

'Yan gudun hijira da za'a rufe sansaninsu
'Yan gudun hijira da za'a rufe sansaninsu

Kamar wadannan yan gudun hijiran ,shima wani dan asalin yankin Michika ya bayyana abun da ya gani a yankunansu da yace ya kamata ayi karatun ta natsu.

To wai ko me ake ciki ne game da batun rufe sansanonin yan gudun hijiran? Sa’adu Bello dake zama jami’in hukumar dake kula da sansanonin yan gudun hijira a shiyar Adamawa da Taraba,wato NEMA, ya bayyana dalilan daukan wannan mataki.

Ga rahoton Ibrahim Abdulaziz.

please wait

No media source currently available

0:00 0:04:23 0:00

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG