Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

AFCON 2021: Senegal Ta Sha Da Kyar, Ghana Ta Sha Kashi


Kasar Senegal ta sha da kyar a wasanta na farko da Zimbabwe na gasar kwallon kafar cin kofin nahiyar Afirka da ake fafatawa a kasar Kamaru.

Wasan na Senegal da Zimbabwe dai ya yi zafin gaske ba kamar yadda aka yi hasashe ba, kafin a minti na karshe Senegal din ta sami zura kwallo ta hanyar fanariti.

Sadio Mane ne ya zura mata kwallon da ya ba ta nasarar doke Zimbabwe din da ci 1-0 a wasan na su na farko na rukunin B.

'Yan wasan Senegal na murnar zura kwallo
'Yan wasan Senegal na murnar zura kwallo

Kasar ta Senegal dai na cikin kasashe na gaba-gaba da ake hasashen za su iya lashe gasar ta bana, kasancewar yanzu haka ita ce ta farko a nahiyar Afirka, a jadawalin mafifitan kasashe ta haujin tamaula na hukumar kwallon kafar duniya wato FIFA.

To sai dai tauraruwar ta bata haska sosai kamar yadda aka zata ba a wasan nata na yau da Zimbabwe, bayan da ta sami tafiya gasar da ‘yan wasa 17 kacal a maimakon 28, sakamakon matsalolin da suka shafi cutar coronavirus da kuma raunuka.

A daya wasan rukunin na B, Guinea ta doke Malawi da ci 1-0, wanda ya ba ta damar samun maki 3, daidai da Senegal.

Guinea ta doke Malawi
Guinea ta doke Malawi

A rukunin C kuma kasar Ghana ta sha mamaki, bayan da Morocco ta doke ta da ci 1-0, yayin da kasashen Gabon da Comoros suke can suna fafatawa a halin yanzu.

'Yan wasan Morocco na murnar zura kwallo
'Yan wasan Morocco na murnar zura kwallo

A jiya Lahadi ne dai aka soma gasar ta bana tare da kasashe 24 a karon farko, inda a wasan farko, mai masaukin baki wato kasar Kamaru ta yi waiwayen baya ta doke Burkina Faso da ci 2-1.

Burkina din ce dai ta soma zura kwallo a ragar Kamaru a wasan nasu na rukunin A, to amma kuma kasar ta Kamaru ta sami bugun fanariti har sau 2, wadanda kuma duk ta sami zura kwallo a cikinsu.

Haka a jiya din, Cape Verde ta yi galabar doke kasar Habasha da ci 1-0 a rukunin na A.

A gobe Talata ne za’a yi karon battar karfe tsakanin Najeriya da Masar, inda kuma Sudan za ta kece raini da Guinea Bissau duk a rukunin D, bayan wasan farko ta rukunin E tsakanin mai rike da kambin gasar wato Algeria da Saliyo.

XS
SM
MD
LG