Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kisan Mutane 100: Afghanistan Ta Ayyana Yau Lahadi Ranar Makoki


Wasu iyayen wasu yaran da harin ya hallaka jigin gawarwakinsu
Wasu iyayen wasu yaran da harin ya hallaka jigin gawarwakinsu

Yayin da ta ke cigaba da tantance barnar da wani dan kunar bakin wake na kungiyar Taliban ya yi ma ta, kasar Afghanistan ta ware yau dinnan don nuna alhini kan wannan danyen aiki, wanda ya yi sanadin rasa rai sama da 100.

Kasar Afghanistan ta ayyana yau dinnan Lahadi a matsayin ranar makoki. An dan saukar da tutoci a fadin kasar da kuma gine-ginen diflomasiyyar Afghanistan da ke fadin duniya, kwana guda bayan da ‘yan bindiga su ka yi amfani da wata motar daukar majinyata mai shake da bama-bamai; wajen kai wani mummunan hari.

Jami’ai sun ce zuwa yau Lahadi, adadin wadanda su ka mutu ya karu zuwa 103, a yayin da kuma wasu 235 su ka ji raunuka a wannan harin da aka kai babban birnin kasar.

Shugaban Afghanistan Ashraf Ghani ya aika da wani sako ta kafar twitter mai cewa, gobe Litini za ta zama ranar da za a mai da hankali wajen samar da abubuwan bukata ga wadanda, a ta bakinsa, “aikin rashin imanin nan na ranar Asabar, wanda aka auna kan farar hula” ya shafe su.

Shugaban ya kuma ce, ta kafar twitter, ranar Talata za ta zama ranar addu’a da karance-karancen Alkur’ani.

Wani harin kunar bakin wake da aka kai da mota ne dai ya bararraka wani wuri mai cinkushe da jama’a a harabar wani ginin gwamnati a birnin Kabul jiya Asabar.

Taliban ta ce ita ta kai harin.

Yayin da Shugaba Ghani ke cewa an kai harin ne kan farar hula, ita kuwa kungiyar Taliban cewa ta yi ta auna jami’an tsaro ne.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG