Accessibility links

Afirka Ta Kudu Ta Tura Sojojin Kasar Su 400 Zuwa Jamhuriyar Afirka Ta Tsakiya.

  • Aliyu Imam

Central African Republic President Re-Elected
Ma’aikatar harkokin wajen Afirka ta kudu tace tura sojojin ya nuna cewa Afirka zata iya magance matsalolinta ba tare da tsoma hanun wasu daga waje ba.

A maraicen lahadin nan ne ofishin shugaban kasar Afirka ta kudu ta bada sanarwar tura sojojin, da tace ta yi tun cikin makon jiya. Sanarwar da Afirka ta kudun ta bayar, tace sojojin zasu taimakawa sojojin kasar Afirka ta tsakiya su kare farmakin da ‘yan tawayen da suke dannawa kan birnin Bangui, wadanda yanzu suke kasa da kilmita metan daga birnin.

Wannan bore na baya bayan nan, yana daya daga cikin irinsu masu yawa da suka addabi wannan kasa mai fama da kuncin talauci, duk da arzikin albarkatun kasa da Allah ya bata, tun lokacin da ta sami ‘yancin kai daga kasar Faransa a 1960. Shugaban kasar na yanzu ya hau mulki ne a 2003 bayan juyin mulki, amma daga bisani yayi takara aka zabe shi kan wannan mukami.

Sanarwar da ofishin shugaban kasar Afirka ta kudu ta bayar, tace sojojinta zasu ci gaba da kasancewa a jamhuriyar Afirka ta tsakiya har zuwa 2018, inda zasu taimaka wajen sake gine rundunar mayakan kasar, kuma za su taimaka wajen kwance damarar ‘yan tawaye, da sake daukar su cikin rundunar mayakan kasar.

Afirka ta kudu tana cikin kasashe masu yawa da suka tura sojoji zuwa Afirka ta tsakiya, da nufin kare gwamnatin kasar daga gamayyar ‘yan tawaye da ake kira Seleka, wadanda tuni suka kama kamar sulusin kasar.

Daya daga cikin korafe-korafen ‘yan tawayen na Seleka, sun hada da cewa gwamnatin kasar ta gaza cika alkawura da ta dauka, ciki harda kwance damar ‘yan tawayen da sake taimaka musu su zauna cikin jama’a. Amma wasu ‘yan tawayen suna bukatar ‘shugaban kasar ya yi murabus, abinda gwamnatin tace ba zata sabu ba.

‘Yan tawayen sun yi alkawarin za su halarci shawarwarin sulhu da aka shirya a wani lokaci cikin makon nan, a Gabon. Amma masu nazari suna shakkar ko akwai hadin kai tsakanin ‘yan tawayen, da zai kai su ga cika alkawarin.
XS
SM
MD
LG