Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Wani jami'in Majalisar Dinkin Duniya Ya Isa Najeriya Zai Kuma Wuce Nijar A Ziyarar kwana hudu,Domin ganin Irin Barnar da Ambaliyar ruwa Ya Haddasa a Kasashen Tsakiya Da Yammacin Afirka.


Wani manomi Ali Danladi cikin ruwa da ya bata masa gona a kusa da wa ni kauyen Ringim,kusa da Dutse,a jihar Jigawa.

Ruwan sama kamar da bakin kwariya da aka tafka ya sa koguna a jamhuriyar Nijar cika,da ma wasu koguna cika su batse,al'amarin da ya shafi mutane kusan milyan daya da rabi. Ya kashe mutane dari uku da saba'in da bakwai.

Laraban nan wani babban jami’in Majalisar Dinkin Duniya ya fara ziyarar kwanaki hudu a Nigeria da jamhuriyar Niger, domin nazarin ambaliyar ruwar data yiwa tsakiya da kuma yammacin Afrika barna.

Ruwan sama kamar da bakin kwarya da aka yi ta tapkawa tasa koguna a jamhuriyar Niger da wasu koguna cika suna batsewa, al’amarin da ya shafi kusan mutane miliyan daya da rabi, ya kashe akalla mutane dari uku da saba’in da bakwai.

Aisha Mohammed stands alongside the remains of a home destroyed by flooding in the village of Rimgim, near Dutse in northern Nigeria, Tuesday, Sept. 28, 2010. Flood waters that rushed through rural Jigawa state now cover about 34 square miles (55 square k
Aisha Mohammed stands alongside the remains of a home destroyed by flooding in the village of Rimgim, near Dutse in northern Nigeria, Tuesday, Sept. 28, 2010. Flood waters that rushed through rural Jigawa state now cover about 34 square miles (55 square k

Haka kuma ambaliyar ruwa tasa an sami bullar annobar ciwon kwalera a Nigeria da Niger, harma sakatariyar harkokin jin kai, Valerie Amos zata gana da kungiyoyin agaji taga yadda suke tinkarar wannan matsala. Kasashen Chadi da arewacin kasar Kamuru suma suna fama da matsalar bullar annobar kwalera.

Tuni kungiyar UNICEF da wasu kungiyoyin kasa da kasa suna agazawa Chadi. A farkon wannan wata na Okotoba nan Chadi ta bada rahoton cewa mutane dubu biyu da dari shidda ne suka kamu da kwalera a kasar,cutar ta kashe mutane dari da goma sha biyu.

Jjamuhuriyar Benin ce tafi fama da ambaliyar ruwar data kashe mutane arba’in da biyu. Gwamnmantin Benin tana taimakon kasashen duniya bayan data ayyana kasar a zaman yankin da bala’in ta yi wa barna matuka. Larabar ce , ake sa ran tawagar wakilan Majalisar Dinkin Duniya mai nazarin bala’i zata isa jamhuriyar Benin.

Shin PI Za Ta Fashe Kuwa Ko Yaudara Ce Kawai?

Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG