Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Afrika ta Kudu Za Ta Gabatar Da Dokar Cinikayyar Hauren Mugun-dawa


Mugundawa Na Hutawa A Afirka ta Kudu
Mugundawa Na Hutawa A Afirka ta Kudu

'Yan majalisar kasar Afrika ta Kudu na duba yiwuwar samar da wata sabuwar doka wacce za ta yunkurin gabatar da wata doka a kwanannan da za ta takaita hadahadar kasuwancin hauren Mugun-dawa.

A farkon shekarar nan ne gwamnati ta nemi a samar da dokar tare da ba da kwanaki 30 domin al'umar kasar su fadi ra'ayinsu dangane da dokar wanda wa'adinsa ya cika a yau Juma'a.

A wannan doka da ake son samarwa, gwamnati na so ta bar cinikayyar cikin gida kan hauren naman dajin na Mugun-dawa da kuma bari a fita da hauruka guda biyu kacal a lokaci guda ga wadanda za su amfani da shi na kashin kansu amma a karkashin wasu tsauraran dokoki.

Hukumar dake kula da muhalli a kasar ta Afrika ta kudu, ta gabatar da bukatar cewa sai an samu cikakken bayanin masu hadahdar haurukan da takardar izni da kuma nau'in hauren da aka sayar.

A shekarar 2009 aka haramta hadahadar sayar da hauren Mugun-dawa a Afrika ta kudu.

Facebook Forum

Hawan Nasarawa, jihar Kano a Najeriya, lokacin da aka gudanar da bukukuwan Sallar Eid el Fitr
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:44 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG