Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Akalla Mutane Hudu Sun Mutu A wani Harin Bam A Afghanistan


Jami'ai a kudancin Afganistan sun ce akalla mutane hudu sun mutu kuma fiye da 30 sun jikkata a fashewar wasu tagwayen boma bomai, a wajen wani bikin baje kayan noma da akeyi duk sabuwar shekara.

Hukumomi sun ce fashewar bam din ya faru ne a yau Asabar a Lashkar Gah, babban birnin lardin Helmand.

Wadanda abin ya faru a gabansu sun ce, karamar fashewar ta farko ta faru ne a cikin wata runfa a filin wasa. Daga nan mutane suka fara gudu zuwa kofar fita, ya yin da bam din na biyu ya fashe a cikin taron mutane.

Wani rahoto ya ce fashewar ta kada Gwamnan Helmand Mohammed Yasin, amma ya sami rauni kadan ne kawai.

Har ya zuwa yanzu babu wanda ya dauki alhakin wannan harin, duk da yake ‘yan kungiyar Taliban suna kai hare-hare irin wannan.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG