Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Akalla Mutane Sha Biyar Suka Mutu a Wani Kunar Bakin Wake


Wani harin kunar bakin wake

Ana cigaba da kai munanan hare-haren bakin wake a Najeriya, ko a yau din nan wani dan kunar bakin wake ya hallaka kansa da mutane 15 ma Fataskum

Wakilin sashin Hausa Haruna Dauda Biu ya aiko mana da rahoto daga karamar hukumar fataskum ta jahar Yoben Najeria wadan da ke nuni da cewar kimanin mutane goma ne suka rasa rayukansu a sakamakon tashin wani bam a wata tashar mota da ke hanyar kano da misalin karfe 12:00 na rana wanda ake kyautata zaton wani fasinja ne ya shiga da bam din cikin wata motar bas wadda tayi lodi zuwa Kano.

Kwanaki Biyu da suka wuce an sami wata fashewar bam a wannan gari na fataskum, ko shekaranjiya ma an sami wata ‘yar kunar bakin wake me kankantar shekaru da ta tada wani bam a yayin da ta afka wa wani wurin da ake hada hadar sayar da wayar hannu ta kashe mutum biyu.

Hukumar Tsaro ta soiji ta fitar da wasu hotuna na wasu motoci da tace ta same su ne ta wajen galabar da ta samu akan ‘yan kungiyar, ta kuma nuna wasu hotuna na wasu yan kungiyar sanye da kayan mata da ke kokarin arcewa.

please wait
Embed

No media source currently available

0:00 0:02:56 0:00
Shiga Kai Tsaye

Shin PI Za Ta Fashe Kuwa Ko Yaudara Ce Kawai?

Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG