Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Akeredolu Na APC Ya Lashe Zaben Ondo


Tambarin Jam'iyar APC

Jam’iyar APC a Najeriya ta lashe zaben gwamnan da aka gudanar na jahar Ondo, inda dan takara Oluwarotimi Odunayo Akeredolu, ya lashe zaben da yawan kuri’u 244,842.

Abokin hamayyarsa na jam’iyar PDP, Eyitayo Jegede, ya samu kuri’u 150, 380, kana dan takarar AD Olusola Oke ya samu kuri’u 126,889.

Zaben na jahar Ondo ya ja hankulan mutane da dama, inda aka rika kai ruwa rana kan wanda zai gaji gwamna mai baring ado, Olusegun Mimiko.

Rahotanni sun ce masu goyon bayan Akeredolu suna ta murna bayan da hukumar zabe jami’in hukumar zabe Prof. Abdulganiyu Ambali ya bayyana sakamkon zaben.

“A wannan zaben babu wanda ya yi nasara babu wanda ya fadi, dukkanmu masu nasara ne, za kuma mu maida hankali ne kan harkar noma.” In ji Akeredolu.

Domin jin karin bayani kan yadda zaben ya kaya, saurari rahoton Hassan Umaru Tambuwal daga Akure, babban birnin jihar Ondo:

please wait

No media source currently available

0:00 0:01:39 0:00

Nijar, Fulani, Wodaabe

Yadda Funalin Wodaabe Suka Gudanar Da Gasar Nuna Kyau A Nijar
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:22 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA

Sauyin yanayi : Yankin Sahel na Afrika

Yadda Sauyin Yanayi Ke Rura Wutar Rikici A Yankin Sahel
please wait

No media source currently available

0:00 0:12:44 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG