Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Akwai Karatun Ta Nutsu Ga Kalamin Buhari Kan Alkalai Game Da Yaki Da Cin Hanci Da Rashawa


Mohammed Buhari

Yanzu haka dai masana harkar shari’a da kuma kungiyoyin kare hakkin Dan Adam a Najeriya, na ci gaba da maida martani game da kalaman da shugaban Najeriya Muhammadu Buhari yayi na cewa alkalai ne ke zama kandagarki na kokarin yaki da cin hanci da gwamnatinsa ke kokari a yanzu.

Sai dai kuma masana na ganin akwai abin dubawa ga kalaman shugaban Najeriyan, ‘daya daga cikin shugabannin kungiyar lauyoyin jihar Taraba barista Idris Abdullahi Jalo, yace akwai alamar karatun ta nutsu ga wannan kalami na shugaban kasa.

Barista Idris yace shi a fahimtarsa ba wai shugaban kasa yana zargin alkalan kotu da kin bashi hadin kai wajen yaki da cin hanci da rashawa a Najeriya, abin nufi anan shine dokar kasa ta tanadar idan ana tuhumar wani da aikata kowanne irin laifi, to dole sai gabatar da shi gaban kuliya a kuma bashi hakkin kai na kare hakkin kansa. Kafin kotu tayi nazarin yanke masa hukunci.

To sai dai kuma ga ‘yan rajin kare hakkin ‘Dan Adam irin su Mallam Musa Jika, ya danganta wannan tafiyar hawainiyar ne da shakulatin bangaro da ga bangaren masu shigar da kara. Inda yake cewa bai kamata ba a daurawa alkalai laifin cewa sune ke kawo jinkiri akan maganar shari’u. ya kuma nemi gwamnati da ta sake duba tsarin da zata taimakawa lauyoyi don tabbatar da sunyi aikin su yadda ya kamata.

Shugaba Buhari ne dai ya koka kan yadda yake ganin alkalai kan iya kasancewa babbar barazana ga cimma burin yaki da cin hanci da rashawa a Najeriya.

please wait

No media source currently available

0:00 0:04:18 0:00
Shiga Kai Tsaye

Gobara A Jihar New York

An Yi Jana'izar Mutane 15 Da Suka Mutu A Gobara A Jihar New York
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:00 0:00
Karin bayani akan Bidiyo

Sauyin yanayi : Yankin Sahel na Afrika

Yadda Sauyin Yanayi Ke Rura Wutar Rikici A Yankin Sahel
please wait

No media source currently available

0:00 0:12:44 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA

Nijar, Fulani, Wodaabe

Yadda Funalin Wodaabe Suka Gudanar Da Gasar Nuna Kyau A Nijar
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:22 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG