Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Akwai Koma Baya Kan Samun Ruwan Sha da Muhalli a Adamawa


Jihar Adamawa

Yayinda da wa'adin da majalisar dinkin duniya ta ba kanta na cimma muradun karni daga shekarar 2000 zuwa 2015 ke cika an soma sharhi akan muradun karni na bakwai da ke karewa kan kiyaye muhalli da ruwan sha shekaru 15 da suka gabata.

Malam Halilu Muhammad shi ne manajan cibiyar samarda ingantacen ruwan sha a yankunan karkara da kuma tsaftace muhalli na jihar Adamawa yace an samu koma baya.

Koma bayan ya faru ne sakamakon kasawar gwamnatin Adamawa na biyan kashi 30 bisa 100 na asusun karo karo na hadin gwuiwa da kungiyoyin majalisar dinkin duniya.

Malam Muhammad yace lallai ba'a cimma muradun bada ingantacen ruwan sha da tsaftace muhalli ba a jihar Adamawa da ma wasu kasashen da yanzu suna son a kara wa'adi. Cikin shekaru bakwai da suka wuce Adamawa bata bada nata kason ba.

A wannan shekarar ce ta fara bada nata kason sannan kasashen waje suka soma bada nasu har ma sun gina rijiyoyin bututu 200 tare da mazagaya 40.

Jihar Adamawa na bukatar sama da nera miliyan 12 domin tara kayan zubar da shara da kuma motocin kwashe shara a fadar jihar da kuma kewaye. Kawo yanzu gwamnatin jihar bata mallaki gwangwanin shara ko motar kwashe shara daya ba.

Babu ingantacen ruwan sha kuma ba'a tsaftace gidajen bahaya dake kasuwaanni ko tashoshin motocin haya.

Ga karin bayani.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:25 0:00

XS
SM
MD
LG