Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Al-Shabab Ta Kashe Gwamnan Lardin Mogadishu.


A harabar asibitin Darishifa a Mogadishu, jiya jumma'a.

Shaidun gani da ido suka ce a daren jumma'a ne 'yan binidgar suka kashe Mohammed Ali Elmi, na yankin da ake kira Galadud dake tsakiyar kasar, a unguwar da ake kira Yaaqshid a Mogadishu.

A Somaliya mayakan sakai na kungiyar al-Shabab sun harbe suka kashe wani gwamnan lardi, tareda da danuwansa. Lamarin ya auku ne a Mogadishu babban birnin kasar.

Shaidun gani da ido suka ce a daren jumma'a ne 'yan binidgar suka kashe Mohammed Ali Elmi, na yankin da ake kira Galadud dake tsakiyar kasar, a unguwar da ake kira Yaaqshid a fadar kasar.

Rahotanni suka ce gwamnan ya kaiwa 'yan uwansa ne ziyara, yayinda 'yan binidgar wadanda suke binsu suka bude musus wuta. Shaidun gani da ido suka ce 'yan binidgar sun gudu daga wurin d a zarar jami'an tsaro suka iso.
Al-shabab ta dauki alhakin kai harin a cikin wata sanarwa data wallafa a wani dandalin internet da take amfani da shi.

Lamarin ya auku ne kasa a sa'ao'i uku. bazyan d a wata mota da aka dankarawa nakiyoyi ta tashi a tsakiyar birnin na Mogadishu ta halaka akalla farar hula uku.

Tun farko a jiya jumma'an, mayakan sakan suka sake kama wani muhimmin gari dake yankin da ake kira Lower Shabelle, bayan da sojojin kiyayen zaman lafiya na kungiyar hada kan kasashen Afirka AU da aka girke a garin suka janye. Mayakan sakan sun shiga garin da ake kira Leego mai tazarar kilomita 120 daga Mogadishu, 'yan mintoci bayan da jerin gwanon sojojin kiyaye zaman lafiya suka fice.

Facebook Forum

Laftanar Janar Farouk Yahaya

Makasan Sheikh Goni Aisami Sun Bata Sunan Sojin Najeriya – Laftanar Janar Farouk Yahaya
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:11 0:00
Karin bayani akan Bidiyo

Shin da gaske NNPP ba ta yi wa Shekarau adalci ba?

Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG