Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Jam'iyya Mai Mulkin Amurka Ta Rasa Kujerar Majalisa Daga Alabama


Dan Takarar Dimukurat Doug Jjones Da Ya Lashe Zaben Sanatan Alabama

Jam'iyyar republican tayi asarar kujerar majalisar dattawa a zaben da aka gudanar a Jihar Alabama.

Dan takarar jam’iyyar Dimukurat mai suna Doug Jones, shine ya lashe zaben da aka yi na maye gurbin kujerar dan Majalisar Dattawa da ke wakiltar jihar Alabama da ke kudancin Amurka.

Abinda yasa wasu da yawa ke ganin nasarar da Doug ya samu wani babban ci baya ne ga jam’iyyar ta 'Republican' tare da nuna tur da alkiblar Shugaba Donald Trump, wanda ya goyi bayan dan takarar jam’iyyar tasu Roy Moore duk da zarginsa da aikata masha'a da wata budurwa 'yar shekaru 14 a lokacin shi kuma yana dan shekaru akalla 30.

Bayan yakin neman zabe mai zafi da suka yi, masu kada kuri’a sun goyi bayan Jones maimakon Moore, ta hanyar kadawa Doug yawan kuri’u da kashi 49 da digo 9 akan kuri’un Roy da ya sami kashi 48 da digo 4.

Sakamakon zaben na nuna cewa, idan aka rantsar da Jones a watan Janairu, rinjayen da ‘yan Republican suke da shi a majalissar dattijai mai kujeru 100 zai ragu, za su koma 51 yayin da ‘yan Democrat za su kasance 49.

Wanda hakan zai haifarwa da Shugaba Trump karin kalubale wajen shawo kan Majalisa don aiwatar da manufofin da ke cikin ajandarsa.

Facebook Forum

Laftanar Janar Farouk Yahaya

Makasan Sheikh Goni Aisami Sun Bata Sunan Sojin Najeriya – Laftanar Janar Farouk Yahaya
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:11 0:00
Karin bayani akan Bidiyo

Shin da gaske NNPP ba ta yi wa Shekarau adalci ba?

Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG